Duniya Labari: Jigo Ya Mutu Awanni 24 bayan Ya Samu Kujera a APC Mai Mulkin Najeriya

Duniya Labari: Jigo Ya Mutu Awanni 24 bayan Ya Samu Kujera a APC Mai Mulkin Najeriya

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Legas ta tabbatar da rasuwar mataimakin sakataren yada labaranta, Karamo Yesiro bayan zabensa a karo na biyu
  • Mai magana da yawun APC ta jihar Legas, Seye Oladejo ya bayyana cewa rasuwar Yesiru babban rashi ne ga jam'iyyar mai mulki tun a 2014
  • APC reshen Legas ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, abokan siyasa da magoya bayansa, tana mai addu’ar Allah Ya ba su hakuri da juriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Jam'iyyar APC reshen Legas ta yi babban rashi awanni 24 bayan kammala taron zaben shugabanni na jiha.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Mataimakin Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar APC a jihar Legas, Karamo Yesiro, ya riga mu gidan gaskiya.

Karamo Yesiro.
Mataimakin sakataren yada labaran APC na jihar Legas, Karamo Yesiro a wata hira da aka yi da shi Hoto: Ado TV
Source: Facebook

Kakakin jam'iyyar APC a jihar Legas ya rasu

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

The Nation ta rahoto cewa Yesiro ya rasu ne sa'o'i 24 bayan sake zabensa a matsayin mataimakin sakataren yada labarai a taron zaben shugabannin APC da ya gudana a filin kwallon Mobolaji Johnson.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na APC a Lagos, Seye Oladejo, ya fitar, ya bayyana mutuwar Yesiro a matsayin babban rashi ga jam’iyyar.

Ya ce mutuwar tasa ta zo a wani lokaci da ake matukar bukatar jajircewarsa, kwarewarsa da kuma kishinsa ga siyasar ci gaba, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.

APC ta fadi halayen marigayi Yesiro

Oladejo ya kara da cewa:

“Bayan an ba shi amanar aiki a Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar APC a jihar Legas, Yesiro ya nuna kwazo, biyayya da kuma cikakken imani da manufofin jam’iyyarmu.”
"Mutum ne mai himma da tawali'u kuma a shirye yake a koda yaushe ya ba da gudummuwa wajen ci gaban APC, ya bar abubuwan da za mu manta da shi."

Ya bayyana cewa duk da cewa wa’adinsa na biyu ya zo karshe cikin gaggawa saboda mutuwa, halayensa na tawali’u, himma da kuma shirinsa na yi wa jam’iyya hidima sun bar kyakkyawan tarihi a zukatan abokan aikinsa a APC.

Kara karanta wannan

Ana azumi Sanata ya gano laifuffukan da ba za su kai 'yan siyasa shiga wutar jahannama ba

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @officialAPCNig
Source: Getty Images

APC ta tura sakon ta'aziyya ga iyalansa

APC ta reshen Legas ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, abokan siyasa da magoya bayansa, tana mai addu’ar Allah Ya ba su hakuri da juriya, Ya ji kan marigayin.

Jam’iyya mai mulki ta jaddada cewa za a ci gaba da tunawa da Karamo Yesiro saboda gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa da karfafa jam’iyyar APC a jihar Legas da kasa baki daya.

Sanatan jam'iyyar APC daga Ribas ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar mazabar Ribas ta Kudu maso Gabas a Majalisar Dattawa, Barinada Mpigi, ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun ce Mpigi, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ayyuka, ya mutu yana da shekaru 64 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Kafin rasuwarsa, yana daga cikin sanatocin Ribas da suka sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262