Bayan Komawa APC, Gwamna Ya Sace Gwiwoyin 'Yan Arewa kan Zaben Shugaban Kasa a 2027
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi tsokaci kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027
- Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana cewa ya kamata a bar yankin Kudancin Najeriya ya kammala shekara takwas kan kujerar mulki
- Gwamnan ya.bayyana cewa bai kamata wani dan Arewa ya fito ya ce zai nemi takarar shugaban kaba ba a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana goyon bayansa ga tsarin karba-karba na shugabancin kasa gabanin zaɓen 2027.
Gwamna Fintiri ya bayyana cewa babu wani ɗan Arewa da ya kamata ya shiga takarar shugaban kasa a 2027.

Source: Twitter
Gwamnan, wanda kwanan nan ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Maris 2023 yayin wata tattaunawa a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito; Gwamna Fintiri ya fadi dalilinsa na komawa APC bayan ficewa daga PDP
Me Gwamna Fintiri ya ce kan zaben 2027?
Ya bayyana cewa ko da yake kowa yana da damar neman kowane matsayi na siyasa, ya dace Kudancin kasar nanya riƙe shugabancin domin tabbatar da adalci da haɗin kan ƙasa.
“Babu ruwan wani ɗan Arewa da batun shugabancin ƙasa a halin yanzu. Lokacin Kudanci ne; ya kamata su kammala shekarunsu takwas, idan har da gaske muke yi game da wannan ƙasa."
"Ya kamata mulki ya riƙa zagayawa domin mu kasance masu lura da yanayin juna a matsayin ’yan’uwa."
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
Daga cikin manyan masu son takarar kujera ta ɗaya a ƙasar akwai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, wanda shi ne ya tsayawa jam’iyyar PDP takara a zaɓen 2023.
Gwamna Fintiri ya goyi bayan Tinubu
Sai dai, gwamnan ya fito fili ya nemi goyon baya ga shugaban ƙasa mai ci, Bola Tinubu, wanda jam’iyyarsa ta APC ta riga ta amince da shi a matsayin dan takararta.
“Me kuma muke buƙata a matsayinmu na kasa? Ba za mu tilasta wa kowa ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa ba, wanda hakan ke nufin za mu ci gaba da tallafa wa mutanenmu wajen yin siyasar cikin gida."
“Kowa ya sani mu tsayayyu ne, kuma idan muka dage, za mu iya yin nasara a zaɓe. Amma waye wannan mutumin da ya fito ya ce yana son takarar shugaban ƙasa a PDP? Kawo yanzu ba mu ga kowa ba."
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

Source: Twitter
Fintiri na goyon bayan karba-karba
A cewar gwamnan, zaman lafiyar wannan ƙasa yana da matuƙar muhimmanci a fagen siyasar Najeriya.
“Har yanzu lokacin Kudanci ne su kammala. Bai kamata dan Arewa halin yanzu ya fito yana neman ofishin shugaban ƙasa ba."
“Idan babu wani ɗan takara, ya kamata mu marawa Bola Tinubu (GCFR) baya domin ya kammala wa’adinsa. Sannan kuma, ya yi ayyuka da dama. Ya kaddamar da kyawawan manufofi waɗanda ke aiki."
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
Gwamna Fintiri ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da watsar da jam'iyyar PDP mai adawa a Najerya domin marawa Bola Tinubu baya a 2027.
Ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin muradun al’ummar Adamawa da hadin kan kasa.
Asali: Legit.ng

