Abin Boye Ya Fito; Gwamna Fintiri Ya Fadi Dalilinsa na Komawa APC bayan Ficewa daga PDP
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yanke shawarar komawa jam'iyyar APC bayan ya fice daga PDP kwanan nan
- Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana cewa bai shiga jam'iyyar APC mai mulki ba domin ya kori wani ko wata daga fagen siyasa
- Gwamnan ya kuma yi kira ga 'ya'yan APC da su karbi sababbin mambobin hannu bibbiyu tare da yi musu alkawarin biyayya ga shugabancin jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi magana kan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Gwamna Fintiti ya bayyana cewa ficewarsa daga PDP zuwa APC mai mulki ba domin ya kawar da kowa ba ne, face domin ya ƙarfafa jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Fintiri ya yi wannan karin haske ne a wurin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Litinin, 2 ga watan Maris a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Kara karanta wannan
Bayan komawa APC, Gwamna ya sace gwiwoyin 'yan Arewa kan zaben shugaban kasa a 2027
Manyan jiga-jigan siyasa na APC da na ɓangaren siyasar Gwamna Fintiri suka haɗu domin ƙarfafa makomar sabuwar APC a jihar, jaridar Businessday ta kawo labarin.
Kwanan nan ne Fintiri ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dukkan tsarin siyasarsa da jami’an gwamnatinsa zuwa jam’iyyar APC a jihar.
Gwamna Fintiri ya hango nasarar Tinubu a 2027
Gwamnan ya bayyana cewa haɗuwar shugabanni daga kowane ɓangare zai ƙarfafa APC a Adamawa, kuma zai tabbatar da gagarumar nasara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dukkan ’yan takarar APC a babban zaɓen 2027.
Ya jinjina wa Shugaba Tinubu da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, bisa goyon bayan abin da ya kira tsari mai kyau na sauya sheƙar.
Hakazalika gwamnan ya yi kira ga mambobin APC da su karɓi sababbin mambobin hannu bibbiyu, inda ya tabbatar musu da biyayya da mika wuya ga shugabancin jam’iyyar.
Fintiri ya yi kira sababbin 'yan jam'iyyar APC
Gwamnan ya buƙaci tsofaffin mambobin PDP da su haɗe cikin APC tare da nuna biyayya da kamun kai, inda ya jaddada muhimmancin biyayya, haɗin kai, da shugabanci mai manufa.
Ya ƙara da yin kiran da a gudanar da tarurruka a matakin unguwanni a faɗin jihar domin ƙarfafa wannan sabon tsarin siyasar.

Source: Twitter
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (Arewa maso Gabas), Mustafa Salihu, ya bayyana taron a matsayin wani babban lamari ga siyasar Adamawa.
Mustafa Salihu ya yaba wa gwamnan bisa ɗauko tsarin siyasarsa ya dawo da shi cikin APC, sannan ya yi maraba da gwamnan zuwa cikin jam’iyyar.
'Yan majalisar dokokin Adamawa sun koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa ya sauya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Rt. Hon. Bathiya Wesley ya fice daga jam'iyyar PDP ne a hukumance tare da wasu mambobin majalisar su 14.
Da yake bayanin dalilinsu na raba gari da PDP, kakakin majalisar ya bayyana cewa rigingimun da suka ki ci, suka ki cinyewa a shugabancin PDP na kasa ne babban dalilin da ya sa suka yanke shawarar barin jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
