Malamai a Siyasa: Sheikh Abdulmuddalib zai Nemi Gwamnan Zamfara a 2027
- Malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdulmuddalib Muhammad Auwal Gusau ya bayyana cewa zai fito takarar gwamnan Zamfara
- Shehin ya bayyana cewa ya riga ya yanki katin zabe da INEC ke yi, yanzu saura masa yin katin jam'iyyar da zai fito takara a 2027
- Sheikh Abdulmuddalib Gusau ya yi karin bayani game da takarar da zai nema ne bayan wata mai tambaya ta masa fatan alheri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Sheikh Abdulmuddalib Muhammad Auwal Gusau ya bayyana cewa zai yi takarar gwamna a jihar Zamfara a 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da muhawara kan ko ya kamata malamai su shiga siyasa ko bai dace ba a Arewacin Najeriya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa malamin ya yi bayanin ne a wani bidiyo da shafin Masjid Imam Ahmad Bin Hambal ya wallafa a Facebook.
Malami zai nemi gwamnan Zamfara
A ranar 13 ga Ramadan, 1447 da ta dace da 2 ga Fabrairun 2026, Sheikh Abdulmuddalib Muhammad Auwal Gusau ya bayyana a wajen tafsiri cewa zai fito takarar gwamna a 2027.
Malamin ya sanar da haka ne yayin da wata mata ta tura tambaya, amma kafin nan ta masa fatan zama gwamna ko Sanatan Zamfara ta Tsakiya.
"A tsaya a gwamnan dai,'
- Inji Malamin yana nuna ya fi fatan zama gwamna a kan Sanata.
Ya kara da cewa:
"Za mu buga fa, da gaske za mu yi fa,"
Malamin ya yi murna da addu'ar da aka yi masa inda ya amsa da "Amin' yana mai cewa da gaske ya ke maganar zai yi takara a 2027.
Kira a yi katin zabe a Najeriya
Sheikh Abdulmuddalib Gusau ya yi kira ga 'yan jihar Zamfara da su fita su yi katin zabe, inda ya ce ta haka ne za su kwaci yancin su a kasar nan.
Shi ma da kansa ya bayyana cewa ya riga ya yanki katin zabe, saura masa katin jam'iyyar da zai yi takara, duk da cewa bai ambaci a wace jam'iyya zai tsaya ba.
Malamin ya ce:
"In ku ka yi katin zabe, ku zabe ni a matsayin gwamnan ku,"
'Kowa ya yi katin zabe, ku zabe ni,'

Source: Facebook
Kira ga malamai su fito takara
Baya ga sanar da shirinsa na yin takara a 2025, Sheikh Abdulmuddalib Gusau ya bukaci sauran malamai su fito takara a jihar.
Ya ce ya kamata sauran malamai su fito takara domin a samu damar tantance wanda zai tsaya daga karshe, inda ya ce watakila ma ya kasance shi ne zabinsu.
Wani malamin Musulunci zai yi takara a Sokoto
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya ayyana cewa zai fito takarar gwamna a jihar Sokoto a 2027.
Malamin ya bayyana haka yayin gudanar da tafsirin watan Ramadan, inda ya ce tura ta kai bango shi yasa ya yanke matsayar.
Ya kara da cewa a da ba shi da niyyar tsayawa takara a jihar, amma saboda wasu abubuwa da suka rika faruwa, dole ya shiga siyasa dumu-dumu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

