"Ba za Mu Iya ba": INEC Ta Yi Magana kan Aika Sakamakon Zaben 2027

"Ba za Mu Iya ba": INEC Ta Yi Magana kan Aika Sakamakon Zaben 2027

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ce ba za ta iya ba da tabbacin cikakken zaɓe 100% 2027 ba
  • Shugaban hukumar, JOASH Amupitan ya ce zaɓen 2027 zai fi kowanne a tarihin Najeriya saboda shirin da aka yi masa
  • Hukumar ta ce tana ƙoƙarin inganta jigilar sakamako da harkokin kayan aikin zane yayin da ya saura watanni a kaɗa kuri'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya ce ba za su iya ba da tabbacin samun zaɓe cikakke 100% a shekarar 2027 ba.

Ya ce wannan rashin tabbaci zai fi shafar tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura kamar yadda ake neman hukumar ta yi don inganta sahihancin zabe.

Kara karanta wannan

Macron ya fadi shirin da Faransa ke yi bayan Amurka da Isra'ila sun kai wa Iran hari

Shugaban INEC ya yi bayani kan aika sakamakon zaɓen 2027 ta na'ura
Shugaban hukumar INEC na kasa, Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Amupitan ya yi wannan bayani ne a wani taron tattaunawa da aka shirya domin jin ra’ayin jama’a kan sahihancin zaɓe.

Kungiyar 'Civil Society Network on Election Integrity' ce ta shirya taron a Abuja a ranar Lahadi, 2 ga watan Maris, 2027.

Shugaban INEC ya magantu kan zaben 2027

Channels ta wallafa cewa a cewar Shugaban na INEC, duk da ƙoƙarin da suke yi, ba za su iya cewa komai zai tafi daidai ba ba tare da tangarda ba.

Sai dai ya jaddada cewa za su yi iya bakin ƙoƙarinsu domin ganin an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

Ya ce ma’aunin nasarar zaɓe ya ta’allaka ne kan abubuwa uku: fara zaɓe a kan lokaci kamar yadda aka sanar, gudanar da shi cikin lumana, da kuma kula da sakamako yadda ya kamata har zuwa ayyana wanda ya yi nasara.

Amupitan ya yi misali da zaɓen kansiloli da aka yi a babban birnin tarayya, inda sakamako ya fito a kan lokaci a yankuna biyar, amma a Kuje, an samu jinkiri a wata mazaɓa har zuwa washegari.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An bukaci shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC ya yi murabus

Abin da Amupitan ya ce kan matsalar zabe

Ya bayyana cewa wasu matsalolin kayan aiki da kuma kura-kuran ɗan adam ne suka haddasa irin waɗannan tangarda, kuma suna aiki tukuru don magance su.

Amupitan ya ce an shirya gudanar da sahihin zabe a 2027
Joash Amupitan (tsakiya) tare da wasu jami'an hukumar INEC Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Shugaban na INEC ya ce duk da cewa ba za su iya ba da tabbacin cikakkiyar nasara ba, suna da ƙarfin tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki.

Abin da kawai ake fargaba shi ne batun tura sakamakon nan take, “a kan lokaci” wato yayin da jama'a ke kada kuri'asu.

Ya yi kwatance da yadda ake tura kuɗi ta manhaja, inda kuɗi kan fita daga asusun mutum nan take, amma mai karɓa ba ya samun saƙon sanarwa sai bayan wani lokaci.

A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne sakamakon ya isa inda ya dace, ko da kuwa ba a lokacin da aka jefa kuri'a ba ne.

Amupitan ya kuma ce sashe na 63 na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanadi kariya idan aka samu matsala ta fasaha, amma a zaɓen da ya gabata ba a samu gazawar tura sakamako ba face jinkiri.

Kara karanta wannan

Zambar N90.4m: Kotu za ta sanar da makomar hujjojin EFCC kan tsohon Shugaban NHIS

Ya ce da yardar Ubangiji zaɓen 2027 zai zama mafi inganci a tarihin ƙasar nN, domin ‘yan Najeriya sun fi wayewa da fahimtar tsarin zaɓe fiye da shekarar 2023.

Ana son Shugaban INEC ya yi murabus

A baya, kun ji cewatsohon dan takarar shugaban kasa, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi watsi da jadawalin zaben 2027, wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar.

Ya bukaci Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi murabus ko kuma ya fuskanci bore daga jama’a gabanin 2027.

Olawepo-Hashim ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja, a matsayin martani ga sabon jadawalin zaben 2027 da INEC ta fitar a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng