"Ba da Jam'iyyu Ba ne"; Atiku Ya Fadi Masu Fafatawa da Tinubu a Zaben 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sake tabo batun zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba zai kasance a tsakanin jam'iyyun siyasa ba
- Hakazalika, ya yi watsi da batun sauya shekar gwamnonin adawa zuwa APC inda ya ce suna yin hakan ne don ceton kansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Atiku ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 ba zai kasance tsakanin jam’iyyun siyasa ba, face fafatawa kai-tsaye tsakanin Shugaba Bola Tinubu, jam’iyyar APC da kuma al’ummar Najeriya.

Source: Twitter
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar a ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026 wadda Paul Ibe ya sanya a shafinsa na X.
Me Atiku ya ce kan masu sauya sheka?
Atiku ya yi waɗannan kalaman ne yayin da yake mayar da martani game da sauya sheƙar gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, inda ya bayyana sauye-sauyen sheƙar siyasa a matsayin sanannen abu a dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ya bayyana cewa kowane ɗan siyasa yana da damar zaɓar tafarkin da yake so, har ma da ’ya’yansa na cikinsa.
A cewar Atiku, kowane mutum, har da ɗansa, wanda ya zaɓi tsayawa tare da ’yan Najeriya maimakon APC, ya zaɓi kishin ƙasa ne fiye da neman abin duniya.
Atiku ya yi watsi da guguwar sauya sheƙar da gwamnonin adawa ke yi a yanzu, inda ya ce hakan ba ya nuna farin jinin APC ba ne, face nuna yanayi na tsoratarwa.
Atiku ya yi zargi kan gwamnatin Tinubu
Ya zargi gwamnatin Tinubu da yin amfani da hukumomi a matsayin makamin tsoratar da abokan hamayya da kuma ƙoƙarin mayar da ƙasar karkashin tsarin jam’iyya ɗaya tilo.
“Wannan gwamnatin tana tsoron gaskiya da riƙon amana. Tana tsoron ingantaccen zaɓe. Tana tsoron jama’a."
- Atiku Abubakar
Ya bayyana cewa babu wata tursasawa ta siyasa da za ta iya ɓoye gaskiyar da ’yan Najeriya ke fuskanta kullum, wadda ta haɗa da yunwa, ƙaruwar talauci, taɓarɓarewar tsaro, da rashin aikin yi.
“Gwamnoni na iya sauya sheƙa domin ceton kansu. Amma miliyoyin ’yan Najeriya na sauya sheƙa ne (daga goyon bayan gwamnati) domin suna son tsira da rayuwarsu. Me APC za ta yi kamfen da shi, yunwa, ƙuncin rayuwa, ko rashin tabbas?”
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Atiku ya ba 'yan Najeriya shawara
Atiku ya buƙaci ’yan Najeriya da kada su ɗauki sauya sheƙar gwamnoni a matsayin samun goyon bayan jama’a, inda ya ƙara da cewa APC ba ta da wata gagarumar nasara da za ta yi kamfen da ita.
Ya gargaɗi ’yan ƙasa da kada su sayar da ƙuri’unsu, inda ya tunatar da su cewa a ƙarshe dai iko yana hannun masu zaɓe ne.
“Kada ku sayar da makomar ku. Kada ku yi gwanjon goben ’ya’yanku. A shekarar 2027, jama’a za su nuna 'yancinsu, kuma ra’ayinsu ne zai yi tasiri."
- Atiku Abubakar
Nadamar Atiku kan jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan rawar da ya taka wajen kafa jam'iyyar APC.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana nadamar kasancewa cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC gabanin zaɓen shekarar 2015.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa yanayin da kasar take ciki a yanzu ya taɓarɓare fiye da yadda yake kafin samar da jam’iyyar.
Asali: Legit.ng


