Babbar Magana: An Bukaci Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, INEC Ya Yi Murabus

Babbar Magana: An Bukaci Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, INEC Ya Yi Murabus

  • Dr. Gbenga Olawepo-Hashim ya yi fatali da sabon jadawalin zaben 2027, wanda ya kayyade lokacin da jam'iyyu za su yi zabukan fitar da yan takara
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce INEC ba ta da hurumin tsarawa jam'iyyu yadda za su tsaida yan takara a zabe mai zuwa
  • Ya yi zargin cewa abubuwan da aka kutsa a jadawalin zaben ya nuna karara cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ba abin yarda ba ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria -Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi watsi da jadawalin zaben 2027, wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar.

Ya bukaci shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi murabus ko kuma ya fuskanci bore daga jama’a.

Kara karanta wannan

Sabon jadawalin zaben 2027 ya fara tayar da kura a Najeriya, ADC ta dura kan INEC

Hashim.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dr. Gbenga Olawepo Hashim Hoto: Olawepo Hashim
Source: Twitter

Leadership ta ce Olawepo-Hashim ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja, a matsayin martani ga sabon jadawalin zaben 2027 da INEC ta fitar ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026.

Olawepo-Hashim ya caccaki hukumar INEC

Ya nuna bacin ransa kan yadda INEC ta gindaya wa'adi da kowace jam'iyyar siyasa za ta gudanar da zaben fitar da dan takara, yana mai cewa wannan ba huruminta ba ne.

Ya ce:

“Ba aikin INEC ba ne ta dora wa jam’iyyu lokacin da za su gudanar da zaben fidda gwani. Wannan ya nuna cewa ba za a iya aminta da shugaban INEC, Amupitan ba.
“Ko dai ya yi murabus ko kuma ‘yan Najeriya za su tashi tsaye su tilasta masa barin ofis. Wadannan mutane ba sa son gudanar da zabe, kuma bai kamata a bar shi ya kara kwana guda a wannan mukami ba, domin ba shi da niyyar shirya sahihin zabe na gaskiya.

Kara karanta wannan

Ta zo gidan sauki: Tinubu ya fadi abin da za a tallata shi da shi a zaben 2027

Ana zargin INEC na shirin taimakon APC

Ya zargi cewa INEC ta shirya wata mankisa a sabon jadawalin zaben, yana mai cewa an tsara shi ne domin amfanar da jam’iyyar APC mai mulki.

A ruwayar Vanguard, Olawepo Hashim ya ce:

“Yana (Amupitan) aiki ne da gangan domin amfanar APC, bayan ya hargitsa sauran jam’iyyun siyasa da suke kokarin warware matsalolinsu a kotu. Wannan rashin adalci ne da kuma mugunta a fili.
“Idan Tinubu ba ya son tsayawa takara, mu fuskanci haka, mu san abin da ya kamata mu yi. Idan ba ya son a yi zabe ne kwata-kwata, ba dole sai ya shirya zabe ba. Za mu dauke shi a matsayin wanda ba ya son zabe.
"Za mu dauke shi a wanda yake son ya makalewa a kujerar mulki. Shugaba Tinubu ba shi ne na farko a Najeriya da ya yi haka ba. Marigayi Janar Sani Abacha ya yi kokarin hakan. Bai so barin mulki ba, ya sa jam’iyyu biyar suka mara masa baya, me ya faru?”

Kara karanta wannan

Saura watanni 11 zabe, Attahiru Jega ya fadi barazanar da ake fuskanta a Najeriya

Shugaban INEC.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Tsohon dan takarar ya ce domin a samu sahihin zabe mai gaskiya a 2027, dole ne a sake fasalin INEC, domin a cewarsa shugaban hukumar ba za a iya dogaro da shi ba.

ADC ta yi fatali da jadawalin zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar hadaka, ADC ta yi fatali da jadawalin zaben 2027 da hukumar INEC ta fitar, ta ce babu adalci a cikinsa kwata-kwata.

ADC ta yi zargin cewa jadawalin na dauke da “makirce-makirce” da aka tsara domin ware jam’iyyun adawa da kuma share wa Shugaba Bola Tinubu hanya ya sake lashe zaben 2027.

Ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci abin da ta kira tsarin zabe na yaudara ba, tana mai cewa tana nazarin matakan da za ta dauka,

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262