Ana Wata Ga Wata: Babbar Kotu Ta Raba Gardama, Ta Yi Hukunci kan Babban Taron PDP na Kasa
- Kwamitin gudanarwa na PDP ta kasa karkashin jagoranci Tanimu Turaki ya yi nasara a karar da aka shigar gaban babbar kotun jihar Oyo
- Kotun ta yanke hukunci a zaman ta na yau Juma'a, inda ta tabbatar da sahihancin babban taron PDP na kasa da aka gudanar a Ibadan
- Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar PDP ke ci gaba da fuskantar rikice-rikicen cikin gida, wanda ke tilastawa manyan jiga-jiganta sauya sheka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo, Nigeria - Babbar kotun jihar Oyo ta tabbatar da sahihancin babban taron jam'iyyar PDP da aka gudanar a birnin Ibadan a shekarar 2025.
Wannan hukunci na nuna cewa shugabannin PDP da aka zaba a wannan taro karkashin jagorancin Tanimu Turaki (SAN) su ne halastattu bisa doka.

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta ce Ladiran Akintola, alkalin Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, shi ne ya tabbatar da ingancin Babban Taron PDP a hukuncin da ya yanke yau Juma'a, 27 ga Fabrairu, 2026.
Kotu ta tabbatar da ingancin taron PDP
Yayin da yake karanto hukunci a karar mai lamba I/1336/2025, alkalin kotun ya amince da gyaran da aka yi a takardar shigar da kara da Musibau Adetunmbi (SAN) ya gabatar a madadin mai kara, Folahan Malomo Adelabi.
Mai shari’a Akintola ya amince da dukkanin bukatu 13 da aka gabatar, inda ya yanke hukuncin cewa taron ya gudana daidai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, da Dokar Zabe ta 2022 (da aka yi wa gyara).
Alkalin ya kafa hujja da sashe na 223(1)(a) da 223(2)(a) na Kundin Tsarin Mulki, Sashe na 82(1) da (2)(a) na Dokar Zabe ta 2022, da kuma sanarwar da aka aika wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a ranar 29 ga Agusta, 2025.
Kotu ta dakil yunkkurin dakatar da shari'a
Ya yanke hukuncin cewa duka matakan da suka wajaba don gudanar da babban taron an bi su yadda ya kamata, ko da INEC ta tura lura ko a’a, don haka taron ya inganta bisa doka.
Kotun ta kuma yi watsi da bukatun dakatar da shari’a da kuma neman dakatar da aiwatar da hukuncin, wadanda Sunday Ibrahim (SAN) ya shigar a madadin Austin Nwachukwu da wasu mutum biyu.

Source: Facebook
Tun da farko, alkalin ya yi fatali da bukatarsu ta shiga cikin karar, yana mai bayyana cewa ba ta da tushe, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.
Gwamnan Bauchi zai bar PDP?
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar PDP wadda ya lashe zaben jihar Bauchi sau biyu a karkashinta.
Bala Mohammed, wanda shi ne kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya bayyana cewa yana nan daram a inuwar da mutanen jihar Bauchi suka zaɓe shi a matsayin gwamna har sau.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar PDP domin dorewar dimokuraɗiyyar Najeriya, wadda ke buƙatar jam’iyyar adawa mai ma’ana da ƙarfi.
Asali: Legit.ng

