2027: Bangaren Kwankwaso Ya Hada kai da Atiku da ADC don Yakar Tinubu

2027: Bangaren Kwankwaso Ya Hada kai da Atiku da ADC don Yakar Tinubu

  • Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi karin haske kan dalin ganinsa a wani taron manema labarai da 'yan adawa suka yi a Najeriya
  • A hirar da aka yi da shi, Buba Galadima ya fadi dalilin hada kai da 'yan bangaren Rabiu Kwankwaso suka yi da su Atiku Abubakar
  • Buba Galadima ya bayyana cewa sun ga alamun da suka nuna cewa Bola Tinubu ya shirya musu makarkashiya a zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - 'Yan NNPP bangaren Rabiu Kwankwaso sun halarci taron da manyan jagororin 'yan adawa a ADC suka shirya a Abuja.

Bayan kammala taron, jigo a NNPP, Buba Galadima ya yi magana kan dalilan da suka sanya mutanen Kwankwaso hada kai da sauran 'yan adawa.

Kara karanta wannan

"Za su iya fadi": Buba Galadima ya hango makomar gwamnatin Tinubu hannun 'yan Najeriya a 2027

Buba Galadima a wani taro
Jagoran NNPP, Buba Galadima a taron NNPP. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

A wata hira da aka yi da shi da DCL Hausa ta wallafa a Facebook, Buba Galadima ya yi korafi da cewa ana kama 'yan adawa ba tare da wasu hujjoji ba.

Dokar zabe ta hada 'yan adawa

Buba Galadima ya ce sun hada kai da sauran 'yan adawa ne saboda dokar zabe da shugaban kasa ya rattabawa hannu kwanan nan.

Ya bayyana cewa manyan korafinsu game da hanyar tura sakamakon zabe, inda ya ce suna bukatar a tura sakamakon zabe ta intanet ta inda ba za a iya tare jami'an INEC a sauya sakamako ba.

Korafi na biyu game da dokar zabe da suka gabatar shi ne hanyar zaben fitar da gwami, Buba Galadima ya ce ba su yarda da fitar da 'yan takara ta tsarin kato bayan kato ko sulhu tsakanin 'yan jam'iyya ba.

'Dan siyasar ya ce an gwada zaben kato bayan kwato a baya bai yi nasara ba, ya zargi APC da cewa:

Kara karanta wannan

Tuna baya: Ɗan Kwankwasiyya ya ce wanda ya zabi Tinubu da APC ba shi ba aljanna

"Domin shugabansu yana tsoron tsayawa zabe, saboda haka sai ya tura 'yan iska su hana zabe shi kenan duk jam'iyyu su rasa 'yan takara na gaskiya sai a ce ya ci ba hamayya."
Yadda aka yi taron 'yan adawa a Abuja
Atiku Abubakar da sauran 'yan adawa a Abuja. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya wallafa a X cewa shugaban NNPP, Dr Ajuji Ahmed ne ya bayyana matsayarsu ga menema labarai bayan kammala taron.

Maganar kama 'yan adawa a Najeriya

Buba Galadima ya bayyana cewa abu na biyu da ya hada su shi ne yadda hukumar EFCC da ICPC ke kama 'yan adawa idan sun yi magana.

Ya ce:

"Su 'yan APC waliyyai ne, ba barayi a cikinsu, su wadanda suke wannan din suma ba barayin ba ne?, Sun fi ma wadanda ake kamawa sata."

Haduwar 'yan NNPP da Atiku Abubakar

Buba Galadima ya ce idan zabe ya zo za su iya janyewa su marawa mutum daya a wakilce su saboda abubuwan da suka gani.

Ya ce wannan taron shi ne na farko a shirin da suke na tunkarar gwamnatin Bola Tinubu domin kawo sauyi a Najeriya a zabe mai zuwa.

APC za ta wayar da kan 'yan kasa

Kara karanta wannan

Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026

A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin APC sun yi taro da jakadun shugaban kasa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa game da 2027.

Jagororin jam'iyyar APC sun bayyana cewa kafin a ci zabe akwai bukatar wayar da kan 'yan kasa, saboda haka dole a shiga gari a nemi mutane.

Manyan APC sun bukaci jakadun shugaban kasar da su shiga kasuwanni da sauran wuraren da jama'a ke taruwa domin wayar da kansu kan nasarorin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng