"Za Su Iya": Buba Galadima Ya Hango Makomar Gwamnatin Tinubu a Hannun 'Yan Najeriya a 2027
- Babban kusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya koka kan halin da gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta jefa 'yan Najetiya a ciki
- Buba Galadima ya yi watsi da ikirarin da gwamnatin ke yi na cewa yanayin rayuwar 'yan Najeriya ya inganta a karkashinta
- Jigon na NNPP ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su korar gwamnatin APC daga madafun iko kamar yadda suka yi wa ta Goodluck Jonathan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi gargaɗi ga gwamnati mai ci ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Buba Galadima ya yi gargadin cewa ’yan Najeriya na iya bayyana fushinsu mai tsanani a akwatin zaɓe a shekarar 2027 idan har matsin tattalin arziƙi da rashin tsaro suka ci gaba da wanzuwa.

Source: Facebook
Buba Galadima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata hira a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv.
Buba Galadima ya soki gwamnatin APC
Jigon na NNPP ya soki manufofin jam’iyyar APC mai mulki, sannan ya yi watsi da iƙirarin cewa yanayin rayuwa ya inganta.
Ya gargaɗi mahukunta da kada su raina fushin jama’a, inda ya buga misali da kama mutane da ake yi saboda bayyana ra’ayoyinsu.
“Duba matasan da ke Kano waɗanda ke zuwa gidajen rediyo don bayyana ra’ayoyinsu. An kama su an tura su gidan yari. Wani lokacin ma alƙalan da aka tursasu kai su gidan yari ne ke yi musu shari’a da daddare."
- Buba Galadma
Buba Galadima ya yi gargadi
Buba Galadima ya ƙara da cewa irin waɗannan ayyukan na iya rura wutar rashin jin daɗi idan ba a shawo kansu ba.
“Wannan fa, abubuwa suna farawa ne kaɗan-kaɗan. Ba ku san yadda za su bunƙasa su zama wani abu daban ba. Kada su yi wasa. Kada su ɗauka cewa ’yan Najeriya wawaye ne kuma ba za su iya martani ba."

Kara karanta wannan
El Rufa'i ya shiga mugun hali hannun ICPC, jini ya rika zuba ta hancinsa ana azumi
- Buba Galadima
Me Buba ya hango kan gwamnatin Tinubu
Yayin da yake kwatanta lamarin da zaɓen shekarar 2015, Buba Galadima ya bayyana cewa ’yan Najeriya sun taɓa nuna shirinsu na korar gwamnati mai ci saboda rashin tsaro, musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Source: Twitter
“Ya kamata su tuna, kuma sun sani fiye da kowa, cewa lokacin da abubuwa suka kai ko da kaso 10 cikin 100 na halin da muke ciki a yanzu a shekarar 2015, ’yan Najeriya sun tashi tsaye suka hambarar da waccan gwamnatin."
“Idan har za a iya cire gwamnatin Jonathan saboda matsalar rashin tsaro a Arewa maso Gabas, me kuke tunanin za a yi wa gwamnatin APC? Ina jin dole ne mu kakkaryata."
- Buba Galadima
Buba Galadima ya yi magana kan Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi magana kan zargin da Amurka ke yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Buba Galadima ya bayyana cewa zargin da ake yi wa Rabiu Kwankwaso ba shi da tushe, yana mai danganta shi da kulle-kullen siyasa.
Jigon na NNPP ya yi watsi da iƙirarin cewa Kwankwaso ya tallafa wa ta’addanci, yana mai cewa tarihin siyasarsa a Kano ya nuna tsayuwa kan akida da bin ka’ida.
Asali: Legit.ng

