Bidiyon Uba Sani Ya Bangaje 'Dan Uwansa Gwamna bayan Taro da Tinubu Ya Jawo Magana
- 'Yan Najeriya da dama sun yi ta surutai bayan yada wani faifan bidiyo da aka yada a kafofin sadarwa bayan ganawar gwamnoni da Bola Tinubu
- An gano Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, yana ture takwaransa na Kogi, Usman Ododo, a wani bidiyo da aka yada
- Lamarin ya faru ne yayin da Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma, ke ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke birnin Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wasu yan Najeriya sun yi martani mai zafi bayan ganin bidiyon wasu gwamnoni na ganawa da manema labarai bayan buda baki da Bola Tinubu.
An dauki Gwamnan Kaduna, Uba Sani a wani bidiyo yana yana ture takwaransa na Kogi, Alhaji Usman Ododo a birnin tarayya a Abuja.

Source: Facebook
Bidiyon Uba Sani yana ture Gwamna Ododo
Bidiyon da tashar Viable TV ta dauka kuma ta wallafa a YouTube ya nuna cewa Hope Uzodimma yana jawabi ga manema labarai a lokacin.
Uzodinma yana jawabi ne kai tsaye ne tare da gwamnan Edo, Monday Okpebholo, a hagu, da gwamnan Kogi, Usman Ododo, a dama.
Lamarin ya faru ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, yayin da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma, ke jawabi ga manema labarai.
Bayan dan lokaci kadan, Uba Sani ya kutsa cikin bidiyon, inda aka gan shi yana ture gwamnan Ododo gefe kafin ya maye gurbinsa a bangaren dama.
Hope Uzodimma ya tsaya domin tattauna wa da manema labarai, inda sauran gwamnoni suka tsaya tare da shi yayin da yake jawabi.

Source: Facebook
Martanin mutane kan abin da ya faru
Yan Najeriya da dama sun caccaki Gwamna Uba Sani kan abin da ya yi inda suke cewa abin takaici ne matuka.
Wasu ko har sauran gwamnoni da ke gefen ma ba su bari musamman Gwamna Monday Okpebholo ya samu rabonsa shi ma.
Gem Onome:
"Okpebholo yana ta kallo kamar yana fahimtar abin da ake cewa."
Chibike Okeakpu:
"Ododo ai daga hannunsa aka yi, ya kamata ya jira umarnin Yahaya Bello."
Jerry Ali:
"Wannan ai ba wani abu ba ne, Gwamna Uzodinma yana cewa duka addinai biyu na azumi, hakan na nuna cewa Uba Sani zai yi magana a madadin Musulmi, ina ga tsarin daukar bidiyon bai da fadin da zai nuna duka gwamnonin a tsaye."
Okafor Chinedu Chidon:
"Gwamnan wadansu ne fa, cin mutunci ne wannan, dole sai Uba Sani ya tsaya kusa da Uzodinma."
AbdurRahmān Aromeh:
"Ban san dalilin haka ba, amma ba zai taba gwada haka ga Yahaya Bello ba."
An yada bidiyon Ododo a gaban Yahaya Bello
A baya, kun ji cewa yan Najeriya a soshiyal midiya sun caccaki gwamnan jihar Kogi wkan kwantar da kai da ya yi yayin gabatar da satifike dinsa na lashe zabe.
An gano zababben gwamnan a wancan lokaci, Usman Ododo, duke a gaban ubangidansa, Gwamna Yahaya Bello bayan nasara a zabe.
Jim kadan bayan nan, sai magoya baya a wajen gabatar da satifiket din suka fara rera wakokin yabo ga gwamnan mai ci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


