'Dan Majalisa Ya Gaji da Rikice Rikice, Ya Rubuta Wasikar Murabus daga Jam'iyyar PDP
- Alhaji Abubakar Abdullahi, dan majalisa a Adamawa ya mika takardar murabus dinsa daga jam'iyyar PDP ga majalisar jihar
- Dan majalisar ya ce ba zai iya ci gaba da zama a PDP ba saboda rikicin jam'iyyar da ya ki ci ya ki cinye wa tsawon lokaci
- Sakataren yada labaran kakakin majalisa ya bayyana cewa akwai karin 'yan majalisa da za su mika takardun murabus dinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Adamawa - Alhaji Abubakar Abdullahi, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Girei a majalisar dokokin Jihar Adamawa, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Alhaji Abubakar ya miƙa wasiƙar murabus dinsa ne ga zauren majalisar dokokin jihar Adamawa yayin zaman majalisar na ranar Talata.

Source: Twitter
'Dan majalisar Adamawa ya fice daga PDP
Kakakin majalisar, Mista Bathya Wesley, wanda ya karanta wasiƙar, ya yi wa ɗan majalisar fatan alheri a jam'iyyar da zai shiga nan gaba, in ji rahoton Punch.
A cikin wasikar murabus dinsa, Alhaji Abubakar ya ce rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP ne ya sanya shi ficewa daga jam'iyyar.
A wata tattaunawa ta musamman da jaridar, babban sakataren yaɗa labarai na kakakin majalisar, Mista Bernard Hyelamada, ya bayyana cewa ana sa ran ƙarin mambobi da za su miƙa nasu wasiƙun murabus ɗin a zaman majalisar na ranar Laraba.
"A ranar Talata, majalisa ta karbi wasika daga mamba mai wakiltar Girei, Alhaji Abubakar Abdullahi. Akwai yiwuwar karin wasu 'yan majalisar da za su turo da wasikunsu a zaman majalisar na ranar Alhamis."
Sauya shekar sanatan Adamawa ta Kudu
Wannan sauyin sheka na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da sanata mai wakiltar Adamawa ta Kudu, Sanata Binos Yaroe, ya bar jam’iyyar PDP.
Dan majalisar dattawan ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar PDP ne saboda samun rarrabuwar kawu a shugabancin kasa, in ji rahoton The Nation.
A cikin wasikarsa, Sanata Binos Yaroe ya bayyana cewa:
"Ina yi wa jam'iyyar fatan alheri a ƙoƙarin da take yi na gyara ɓarnar da ta yi wa kanta."

Source: Original
Atiku da takarar Sanata Yaroe a 2027
Bincike ya nuna cewa Sanata Yaroe na shirin komawa jam'iyyar ADC ne domin tabbatar da ya sake samun takara ba tare da hamayya ba.
Sanata Yaroe ya fito ne daga mazabar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda ake sa ran zai tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ta ADC.
Wata majiya ta bayyana cewa Atiku Abubakar ya ba Sanata Yaroe tabbacin cewa zai koma majalisar dattawa a 2027.
Majalisar Adamawa ta kara wa gwamna karfi
A wani labari, mun ruwaito cewa, majalisa ta amince gwamnan Adamawa ya nada shugaban riko idan Sarki ko Hakimi ya kwanta rashin lafiya ko kuma ya gaza aiki.
Hakan na kunshe ne a kudirin da Majalisar ta amince da shi wanda ya yi wa dokar nadawa da sauke sarakuna gyara a jihar Adamawa.
Dokar ta tanadi cewa duk wanda aka nada a matsayin Sarki ko Hakimin na rikon kwarya zai sauka idan basaraken ya samu lafiya ko ya dawo aiki.
Asali: Legit.ng

