Tashin Hankali: 'Yan bindiga Sun Farmaki Peter Obi, An Yi Yunkurin Kashe Shi a Benin
- Peter Obi da shugabannin jam'iyyar ADC sun tsallake riji da baya bayan wasu mahara sun kai musu farmaki a birnin Benin dake Edo
- Yunusa Tanko ya bayyana cewa maharan sun biyo su har gidan John Odigie-Oyegun inda suka bude wuta tare da lalata motoci
- An kai wannan hari ne yayin da manyan yan siyasar suka hallara domin bikin shelar komawar Olumide Akpata zuwa jam'iyyar ADC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Edo - Kodinetan ƙungiyar "Obidient Movement" na ƙasa, Yunusa Tanko, ya yi zargin cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi a birnin Benin.
Tanko ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin an dauko hayarsu don kisan kai ne suka farmaki Peter Obi tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan
An fara nuna yatsa ga Tinubu da 'yan bindiga suka farmaki Obi, tsohon shugaban AP

Source: Twitter
An farmaki Peter Obi da kusoshin ADC
Lamarin ya faru ne lokacin da Peter Obi da sauran shugabannin jam'iyyar ADC suka halarci taron shelar komawar Barrister Olumide Akpata zuwa jam'iyyar ta ADC, in ji rahoton The Sun.
Kamar yadda Yunusa Tanko ya wallafa a shafinsa na X, wasu mahara dauke da makami sun biyo su tun daga sakatarayar jam'iyyar ADC har zuwa gidan tsohon gwamnan jihar Edo, Chief John Odigie-Oyegun.
Maharan sun buɗe wuta a jikin ƙofar gidan sannan suka lalata motoci da dama a wani abu da Tanko ya bayyana a matsayin yunƙurin kisan gilla.
Yunusa Tanko ya bayyana cewa:
"Sun yi harbi a jikin ƙofar gida sannan suka lalata motoci da dama a wani abu da ya zama yunƙurin kisan gilla ga rayuwarmu."
Abin da ya kai Peter Obi Edo
Ya ƙara da cewa wannan hari babban barazana ne ga dimokuraɗiyyar Najeriya, musamman ganin yadda aka kai wa Peter Obi da Chief John Odigie-Oyegun hari yayin da suke gudanar da harkokinsu na siyasa.
Tawagar Peter Obi tana birnin Benin ne domin shaida komawar Olumide Akpata zuwa jam'iyyar ADC, kamar yadda rahoton ya nuna.
Akpata dai shi ne ɗan takarar gwamna a zaɓen baya-bayan nan na jihar Edo wanda Gwamna Monday Okpebholo ya yi nasara.

Source: Twitter
"Dimokuradiyya na cikin hadari" - Tanko
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan ko an sami rauni a tsakanin tawagar Peter Obi, amma rahoton ya nuna cewa dukkan jiga-jigan sun tsallake riji da baya.
Jami'an tsaro ba su riga sun fitar da sanarwa a hukumance kan wannan harin ba, amma Yunusa Tanko ya yi ikirarin cewa "dimokuradiyya tana cikin hadari."
Wannan lamari ya sa magoya bayan Peter Obi a fadin ƙasar nan shiga cikin yanayi na fargaba da kuma taya tsohon dan takarar shugaban kasar jajen abin da ya faru.
Karanta sanarwar Tanko a nan kasa:
An farmaki sakatariyar jam'iyyar ADC
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bangar siyasa sun farmaki hedikwatar jam’iyyar ADC a Benin inda suka fasa tagogi tare da kokarin kona ginin.
Shugaban jam’iyyar Kennedy Odion ya zargi abokan hamayya da kokarin tsoratar da su domin su fice daga takarar zaben shekarar 2027.
Rundunar yan sanda ta tura karin jami’an tsaro zuwa titin Ogbelaka bayan rahoton barnar da aka yi wa tutocin jam’iyyar da wasu kayayyaki.
Asali: Legit.ng

