An Fara Fahimtar Wadanda APC za Ta Zaba Shugabannin Jam'iyya na Kasa a Babban Gangami
- Alamu sun fara nuna mutanen da APC za ta yi aiki da su a matsayin shugabanninta yayin da ake shirin babban taron jam'iyya
- A yanzu haka, Nentawe Yilwatda da sauran jagororin jam'iyya na kasa za su iya ci gaba da rike mukamansu kamar yadda alamu ke nunawa
- Ana ganin jam'iyyar za ta yi amfani da tsarin masalaha wajen samar da shugabannin da za su jagoranci jam'iyya a matakin kasa a taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Alamu sun nuna cewa jam’iyyar APC na shirin barin Farfesa Nentawe Yilwatda ya ci gaba da zama Shugabanta na 'kasa.
Ana sa ran cewa Sanata Ajibola Basiru zai ci gaba da zama Sakataren Ƙasa a babban taron ƙasa da za a yi a ranakun 27 da 28 ga Maris 2026.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa manyan jam’iyyar da suka nemi a sakaya sunayensu sun tabbatar da yawan mutanen da za su iya ci gaba da rike mukamansu.
Masu son rike shugabancin jam'iyya APC
Jaridar The Sun ta wallafa cewa cewa kusan mutum 20 daga cikin masu riƙe da mukamai a kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na neman a sake zaɓensu.
Tun yanzu, har, sun fara ganawa da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki domin neman goyon baya kafin babban taron.
Mataimakin Sakataren tsara jam’iyya na 'kasa, Nze Duru, ya tabbatar da cewa shugabanni sun amince da tsarin maslaha domin ƙarfafa haɗin kai, rage sabani da tabbatar da zaman lafiya a wajen taron.

Source: Facebook
APC ta kammala zaɓukan mazabu da ƙananan hukumomi a mafi yawan jihohi bisa sabon jadawalin da ta fitar, sai kaɗan daga cikin jihohin da aka ɗage.
Babban taron na Maris ne zai kammala da zaɓen sababbin yan kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC.
Ana shirin babban taron APC na kasa
Kwamitin shirya taron, ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ne aka ɗora wa alhakin kula da dukkan shirye-shiryen.
Bisa tanadin kundin tsarin mulkin APC na Maris 2022 da aka yi wa jami’an jam’iyya na yin wa’adi na shekaru huɗu, kuma ana iya sake zaɓensu sau ɗaya tak.
Wata majiya a APC ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna yana goyon bayan a bar Yilwatda da Basiru su ci gaba da riƙe mukamansu.
An ce an kusan tsayar da magana a kan batun shugabanci da sakataren ƙasa na APC yayin da tattaunawa kan sauran mukamai ke gudana.
Wata majiya ta ce a baya akwai shakku kan a bar Basiru ya ci gaba saboda shi da Shugaban ƙasa duk daga yankin Kudu maso Yamma suke.
APC ta hana saya wa Tinubu fom
A baya, kun samu labarin cewa jam'iyyar APC ta yi martani bayan wasu matasa sun hada miliyoyin Naira domin saya wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu fom din takara.
Shugaban jam'iyyar ya mika godiya ga matasan da suka saye fam din, sai dai ya gargadi masu yunkurin cewa za su cigaba da yin hakan gabanin zaben 2027.
Shugaban APC na kasa, Nentawe Goshwe Yilwatda, ne ya bayar da umarni hana saya wa shugaban kasa fom din takarar 2027 a lokacin da ya karbi N100m na saya wa kudin fam.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


