NNPP Ta Yi Zargin ana Haɗa Baki da Jami'an Tsaro ana Cafke Ƴaƴanta a Kano
- Jam'iyyar adawa ta NNPP a Kano ta yi Allah-wadai da kama 'daya daga cikin 'ya'yanta, Aiha K. Nass da jami'an tsaro suka yi
- Sakataren yada labaran jam'iyyar, Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ne ya bayyana haka a Kano, inda ya ce ba a kyautawa
- Ta bukaci hukumomin tsaro su guji son kai a tsarin dimokuraɗiyya ko kuma daukar bangare a yayin gudanar da aikinsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi Allah-wadai da kama daya daga cikin 'ya'yanta, Aiha K. Nass, da hukumomin tsaro suka yi a Kano.
A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar 22/02/2026, Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar a Kano, Injiniya Ibrahim Karaye, ya ce wannan abin takaici ne.

Source: Twitter
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ibrahim Karaye ya bayyana cewa NNPP ba za ta abin da da irin wannan cin kashi ba.
NNPP ta soki kama 'danta a Kano
Ibrahim Karaye ya tabbatar wa Legit cewa suna takaici da yadda gwamnatin Kano ta juya masu baya bayan ta sauya sheka.
Ya ce:
"Abin da ya ba mu mamaki shi ne, gwmanatin da aka kawo ta saboda adawa, gwamnatin da aka kawo ta saboda an yaki wata gwamnati, sai kuma abin mamaki, da da su muke zuwa idan an kama mutane mu je mu karbo su, amma abin takaici sun zo, sun hada kai da wasu grubatattu daga cikin jami'an tsaro, suna zuwa suna kama mana mutane."
Da yake magana a hedikwatar jam’iyyar, Injiniya Karaye ya ce NNPP na Allah-wadai da abin da ya kira kama 'daya daga cikin 'ya'yanta ba bisa doron adalci ba.
Ya ce:
“Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi Allah-wadai da Aiha K. Nass da hukumomin tsaro suka yi a Kano.”
Kiran NNPP ga jami'an tsaro a Kano
Ya kara da cewa jam’iyyar na kira ga dukkannin hukumomin tsaro da su guji nuna son kai a cikin tsarin dimokuraɗiyya.

Source: Twitter
A cewarsa:
“Muna kira ga dukkannin hukumomin tsaro da su daina duk wani mataki na son kai a cikin yanayin dimokuraɗiyya.”
Jam’iyyar ta bayyana cewa a kasa mai bin tsarin dimokuraɗiyya, ya kamata a mutunta hakkokin ‘yan kasa tare da tabbatar da gaskiya da adalci a duk wani mataki da ake dauka.
Haka kuma, NNPP ta bukaci a saki Aiha K. Nass ba tare da ɓata lokaci ba saboda ‘yan kasa na da ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin shiga kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa.
Sakon Kwankwaso ga wadanda suka bar NNPP
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce kofarsa a bude ta ke ga dukkanin wadanda suka sauya sheka tare da gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Gwamna Abba ya bayyana ainihin dalilinsa na komawa APC a gaban Shettima
Ya bayyana haka ne a wani sako da ya tura ga masoya da magoya bayan tsarin Kwankwasiyya da ke tsarin daka wajen tabbatar da dorewar siyasarsu.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kara da bayyana takaici a kan yadda aka dauke gwamnatin Kano da suka yi wa wahala zuwa APC da Gandujiyya.
Asali: Legit.ng

