Ana Wata ga Wata: APC Ta Hana Saya wa Tinubu Fom din Takarar 2027

Ana Wata ga Wata: APC Ta Hana Saya wa Tinubu Fom din Takarar 2027

  • Jam'iyyar APC ta yi martani bayan wasu matasa sun hada miliyoyin Naira domin saya wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu fom din takara
  • Shugaban jam'iyyar ya mika godiya ga matasan da suka saye fom din, sai dai ya gargadi masu yunkurin cewa za su cigaba da yin hakan
  • Wani daga cikin shugaban matasan jihar Kogi da suka ware kudin sayen fom din ya yi karin haske game da kudin da suka tara wa Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Kwamitin NWC na jam’iyyar APC ya umarci ƙungiyoyi ko daidaikun mutane da ke shirin sayen fom ɗin tsayawa takara domin sake zaɓen shugaba Bola Tinubu a 2027 da su dakata.

A wani taron da aka gudanar a Abuja bayan matasa sun saye fom din takara ga shugaban kasar, jam'iyyar APC ta ce daga yanzu babu buƙatar hakan.

Kara karanta wannan

2027: Matasa sun yi karo karo, sun tara N100m don saya wa Tinubu fom ɗin takara

Shugaban kasa Bola Tinubu a Aso Rock Villa
Bola Tinubu na magana a fadar shugaban kasa. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

APC ta hana saya wa Tinubu fom

The Sun ta rahoto cewa shugaban APC, Nentawe Goshwe Yilwatda, ne ya bayar da umarni hana saya wa shugaban kasa fom din takarar 2027.

Farfesa Yilwatda ya fadi haka ne a lokacin da matasan Jihar Kogi, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Usman Ododo, suka miƙa takardar kuɗi ta Naira miliyan 100 domin sayen fom ɗin takarar shugaban ƙasa ga Bola Tinubu a Abuja.

Nentawe ya ce duk da cewa wata ƙungiyar matasa ta gabatar da takardar alƙawarin Naira miliyan 200 domin sayen irin wannan fom, har yanzu ba su cika alƙawarin ba.

Ya jaddada cewa babu buƙatar wata ƙungiya ko mutum ya ƙara wahalar da kansa da shirin biyan wani ƙarin kuɗi domin sayen fom ɗin sake tsayawa takara wa shugaba Tinubu.

Punch ta wallafa cewa shugaban APC ya ce:

“Wannan shi ne rukuni na biyu da ya nuna irin wannan ƙuduri. Na farko ya yi alƙawari amma bai cika ba. Waɗannan sun yi alƙawari kuma sun cika.

Kara karanta wannan

Barau Jibrin ya fito da alamun nasarar Tinubu, Abba da sauran 'yan APC a 2027

"Saboda haka, ina sanar da cewa kar wani ya ƙara kawo kuɗi domin sayen fom ga mai girma Shugaban kasa, domin matasan Kogi sun riga sun saya tun da wuri,”
Yadda aka sayawa Bola Tinubu fom din takara
Lokacin mika kudin fom din takara ga Bola Tinubu. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Bayanin 'yan APC daga Kogi

Yayin da yake kare sayen fom ɗin, gwamna Ododo ya ce babu wata gwamnati da ta ba matasa dama kamar yadda mai girma shugaban kasa Tinubu ya yi a Najeriya.

Jagoran matasan Kogi, Mista Mundi, ya yi alƙawarin bayar da wani adadi na kudi idan jam’iyyar ta ƙara farashin fom, yana cewa:

“Ina tabbatar muku cewa mun riga mun tanadi fiye da Naira miliyan 100 idan har an ƙara sama da adadin da muka bayar.”

Matasa sun sayawa Tinubu fom

A wani labarin, kun ji cewa wasu matasa a jihar Kogi sun hada kudi a tsakaninsu har Naira miliyan 100 domin sayen fom din takarar 2027 ga Bola Tinubu..

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda ne ya karbi kudin ta hannun gwamna Usman Ododo a wani taro da aka yi a Abuja.

Nentawe Goshwe Yilwatda ya bayyana jin dadinsa game da kokarin da matasan suka yi, ya ce matasa na bayar da gudunmuwa maimakon neman tallafi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng