Dokar Zabe: An Kara Yawan Kudin Kamfen, 'Dan Takarar Shugaban Kasa zai Kashe N10bn
- Sabuwar dokar zaben kasar nan ta kara yawan kudin yakin neman zabe da mai neman shugaban kasa zai iya kashewa a wajen kamfe
- Wannan na nufin an kara yawan kudin da za a kashe a wajen yakin neman zaben Shugaban kasa gabanin 2027 da ke karatowa
- Baya ga kamfen na shugaban kasa, dokar zaben ta kayyade kudin neman takarar gwamnoni, Sanataci da na 'yan majalisun wakilai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya yi karin haske a kan sabuwar dokar zaben da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.
Sanata Bamidele ya kuma yi magana a kan karin kudin kamfen da aka samu a sabuwar dokar, kamar yadda Sashe na 92(1-8) ya tanada.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa a cewarsa, an daga iyakar kudin takarar shugaban kasa daga N5bn zuwa Naira biliyan 10.
An kara kudin kamfen a dokar zabe
Hakazalika, an kara kudin neman takarar gwamna daga N1bn zuwa N3bn sai kuma na Sanata daga Naira miliyan 100 zuwa miliyan 500.
A cikin sabuwar dokar zaben, ‘yan Majalisar Wakilai za su kashe daga miliyan 70 zuwa miliyan 250 a kamfen; na ‘yan Majalisar Jiha daga miliyan 30 zuwa miliyan 100.
Dokar ta bayar da dama ga masu neman kujerar kansilolin yankin birni su kashe daga miliyan 30 zuwa miliyan 60; yayin da sauran kansiloli ya tashi daga miliyan biyar zuwa miliyan 10.
Abin da doka ta tanada kan sayen kuri'a
A karkashin Sashe na 125(1-2), an tsaurara hukunci kan sayen kuri’a, da murde sakamakon zabe.
Duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci daurin shekaru biyu ko tarar kudi tsakanin N500,000 zuwa N2m ko duka biyun.

Kara karanta wannan
Sabuwar dokar Tinubu ta zo da alheri, kasafin gwamnatoci zai karu da tiriliyoyin Naira
Bamidele ya kuma ce Sashe na 74(1) ya wajabta wa Kwamishinan Zabe na Jiha (REC) ya fitar da kwafin sahihin takardu cikin awa 24 bayan biyan kudin da ya dace.

Source: Facebook
Majalisar Tarayya ta kuma bayyana cewa dokar ta samar da asusun musamman ga INEC, wajabcin tura sakamakon zabe ta IReV da sauransu.
Sabon tsarin ya wajabta amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu kada kuri’a, tare da daurin shekaru biyu ga duk wani REC da ya boye muhimman takardu.
Haka kuma, Sashe na 60(3) ya tanadi tura sakamakon zabe kai tsaye zuwa dandalin IReV, yayin da Sashe na 60(6) ya kayyade daurin watanni shida ko tarar N500,000 ga duk jami’in zabe da ya hana tura sakamakon kai tsaye.
An sanar da sakamakon zaben Abuja
A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar APC ta lashe kujerar shugabancin Kuje a zaben kananan hukumomin Abuja da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
A sakamakon da ta fitar a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026, hukumar INEC ta tabbatar da cewa Danjuma Shekwolo na APC ya samu kuri’u 17,269, ya doke jam'iyyar PDP da APGA.
Baturiyar zabe, Farfesa Nkiruka Odoh, ta sanar da cewa Shekwolo ya cika sharuddan doka kuma an tabbatar da nasararsa a zaben da aka gudanar a karshen mako.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
