Kwankwaso Ya Hadu da Gawuna bayan Zuwa Gidan Shekarau a Kano
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da tsohon dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna
- Hakan na zuwa ne bayan madugun Kwankwasiyya ya kai ziyara gidan tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau bayan rashi da aka masa
- Kafin tafiya filin jirgin sama da niyyar fita daga Kano, Rabiu Kwankwaso ya karbi baki da dama da suka hada da malamai da 'yan siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da Nasiru Yusuf Gawuna a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Gawuna cikakken dan APC ne da ya yi takarar gwamna a karkashin jam'iyyar a zaben shekarar 2023, kuma na hannun daman Abdullahi Ganduje.

Source: Facebook
Hadimin Rabiu Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa bidiyon tambayar da jagoran NNPP ya yi wa Gawuna a shafinsa na Facebook.
Kwankwaso ya hadu da Gawuna
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da Dr Nasiru Yusuf Gawuna a filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano, Kano.
Bidiyo ya nuna Rabiu Kwankwaso na mika wa Gawuna hannu su gaisa amma ya ki karbar hannun ya tsuguna kasa ya gaishe da jagoran NNPP.
Haka zalika sauran da ke tafiya tare da Nasiru Gawuna sun tsuguna sun gaishe da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a filin jirgin saman.
Kwankwaso ya tambayi Gawuna:
"Kana lafiya, ya gajiya, sannunku fa, Abuja ko Legas?"
Sai Gawuna ya ce:
"Abuja, lallaboi."
Kwankwaso ya ziyarci Shekarau
Kafin haduwarsa da Nasiru Gawuna, Rabiu Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya ziyarci gidan Malam Ibrahim Shekarau.
Kwankwaso ya ce:
"A yau a Kano, na kai ziyarar ta’aziyya ga mai girma Sanata Ibrahim Shekarau, bisa rasuwar babban yayansa, Malam Dahiru Shekarau.
"Tare da ni akwai mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo.
"Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya ba shi Aljanna, Ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan rashi."

Source: Facebook
Wasu da suka ziyarci Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso, ya karɓi bakuncin Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, wanda ya kawo masa ziyarar girmamawa inda ya yi masa addu’a tare da roƙon Allah ya albarkaci jagorancinsa da ci gaban jihar Kano da Nijeriya.
Haka zalika, jagoran jam’iyyar NNPP ya karɓi ziyarar girmamawa daga iyalan marigayi Dan Zago, inda ya roki Allah ya jikansa da rahama, ya sanya aljanna ce makomarsa.
A daya bangaren, Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi ziyarar girmamawa daga tsohon ɗan majalisar wakilai da ya wakilci Gabasawa, Nasiru Auduwa tare da tawagarsa.
Majalisar shari'a ta kare Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa majalisar shari'ar Musulunci ta Najeriya ta kare Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bisa zargin da aka masa a kasar Amurka.
Majalisar ta bayyana cewa akwai rashin adalci a zargin da aka yi wa Kwankwaso game da tauye hakkin addini, musamman lura da cewa shi kadai aka ware.
Ta kara da cewa abin takaici ne yadda Amurka ta dogara da wasu bayanai marasa inganci wajen daukar mataki mai muhimmanci.
Asali: Legit.ng


