Tinubu Ya Yi Magana kan Zabukan Kano da Abuja, Ya Kira Sunan Wike Musamman
- Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan rawar da ya taka wajen nasarar APC a zabuka
- APC ta samu gagarumar nasara a zaben kananan hukumomi shida na Abuja tare da wasu zabukan cike gurbi a Rivers da Kano
- Tinubu ya bukaci zababbun shugabanni su yi aiki da kaskantar da kai, yana mai yabawa INEC da jami’an tsaro kan gudanar da zaben cikin lumana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana bayan APC ta samu nasara a wasu zabukan da aka gudanar a karshen mako.
Tinubu ya yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa nasarorin da ya samu a Abuja wanda ya ce sun haifar wa APC ribar siyasa.

Source: Twitter
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X.
Yadda APC ta yi nasara a wasu kujeru
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar da zaben ne a dukkan kananan hukumomin Abuja, tare da zabukan cike gurbi a mazabu daban-daban a Rivers da Kano.
APC mai mulki ta samu gagarumar nasara inda ta lashe mafi yawan mukaman da aka fafata a zaben.
Tinubu ya taya zababbun yan takarar APC murna
Shugaban kasa ya taya dukkan wadanda suka yi nasara murna, tare da yabawa shugabannin APC na kasa da na Rivers da Kano bisa nasarorin da jam’iyyar ta samu a rumfunan zabe.
Tinubu ya kuma yaba wa INEC, jami’an tsaro da masu kada kuri’a kan yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da nasara.
Ya bukaci wadanda aka zaba su yi aiki da “kaskantar da kai, kishin kasa da sadaukarwa,” yana mai cewa amincewar da al’umma suka ba su wata amanar Allah ce.

Source: Facebook
Tinubu ya yi kira ga hukumar zabe a Najeriya
Shugaban ya jaddada cewa nasarar zaben na kara karfafa dimokuradiyya da cibiyoyinta, tare da kira ga INEC da ta ci gaba da inganta tsarin zabuka domin kara tabbatar da sahihanci.
Tinubu ya kuma bayyana cewa kokarin da Wike ya yi a Abuja ya haifar wa APC ribar siyasa, duk da cewa ministan mamba ne na jam’iyyar PDP.
Ya kara da cewa dimokuradiyya na kara karfi ne ta hanyar shiga fafatawa da gasa cikin gaskiya da bin doka, yana mai yabawa dukkan ‘yan takarar da suka nuna jarumtaka da ladabi.
Abba Kabir ya yabawa hukumar zabe, APC
Mun ba ku labarin cewa gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya yi magana bayan gudanar da zaben cike gurbi da aka yi a wasu yankunan jihar.
Gwamna Abba ya yaba wa hukumar zaben jihar da jami’an tsaro kan gudanar da zaben cike gurbi cikin kwanciyar hankali.
Ya ce an gudanar da zaben cikin tsari da lumana a mazabun cikin birnin Kano da Ungogo, lamarin da ya nuna balagar siyasa da hadin kan jama’a.
Asali: Legit.ng

