An Buga Ta: INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Karamar Hukumar Birnin Abuja
- Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC na ci gaba da sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da ake yi a Abuja
- Hukumar ta ayyana Christopher Maikalangu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar birnin Abuja
- Wakilan jam’iyyu sun yaba da sahihancin tattara sakamakon, suna cewa hakan alama ce ta shirin APC na shekarar 2027
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi a Abuja.
Hukumar ta sanar da cewa Christopher Maikalangu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben shugaban karamar hukumar birnin Abuja (AMAC).

Source: Original
APC ta yi nasara a zaben birnin Abuja
Jami’in tattara sakamakon zaben na AMAC, Andrew Abue, ya ce Maikalangu, wanda shi ne shugaban karamar hukumar mai ci a yanzu, ya samu kuri’u 40,295 cikin kuri’u 62,861 da aka tantance a matsayin ingantattu, cewar Punch.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta zo ta biyu da kuri’u 12,109, yayin da jam'iyyar adawa ta PDP ta samu kuri’u 3,398.
A cewarsa, kuri’u 2,336 ne aka soke, inda jimillar kuri’un da aka kada suka kai 65,197, haka kuma, an bayyana cewa masu rajista a AMAC sun kai 837,338, yayin da aka tantance masu kada kuri’a 65,676.
Abue ya ce:
“Tun da Maikalangu na APC ya cika sharuddan doka, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya zama zababben shugaban karamar hukumar.”

Source: Getty Images
Yawan jam'iyyu da suka fafata a zaben Abuja
Jam’iyyu 12 ne suka fafata a zaben da aka gudanar a jiya Asabar, ciki har da APGA da YPP da kuma NNPP da sauransu a Abuja.
Da yake magana bayan sanar da sakamakon, wakilin APC a cibiyar tattara kuri’u, Gambo Babale, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben, yana cewa an bi dukkan matakan da suka dace.
Ya ce nasarar da APC ta samu alama ce da ke nuna cewa jam’iyyar na da kwarin gwiwar tunkarar zaben 2027, cewar The Guardian.
Haka kuma, wakilin YPP, Abdullahi Ibrahim, ya bayyana tsarin tattara sakamakon a matsayin mai gaskiya, inda ya taya wanda ya yi nasara murna.
An kuma ruwaito cewa wakilan jam’iyyun ADC, APC, APGA, YPP da NNPP sun sanya hannu kan takardun sakamakon a cibiyar tattara kuri’u.
An sanar da sakamakon zaben Kwali a Abuja
Mun ba ku labarin cewa Hukumar INEC ta ayyana cewa Daniel Nuhu na jam'iyyar APC ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Kwali da kuri'u 17,032.
Dan takarar na APC ya doke Haruna Pai na PDP wanda ya samu kuri'u 8,575 a zaben na ranar Asabar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da aka gudanar.
Zuwa yanzu jam'iyyar APC ta lashe kananan hukumomi uku da suka hada da AMAC da Bwari da kuma Kwali a zaben birnin Abuja da aka gudanar.
Asali: Legit.ng

