Kwali: APC Ta San Matsayinta bayan INEC Ta Fadi Sakamakon Zaben Ciyaman a Abuja
- Hukumar INEC ta ayyana cewa Daniel Nuhu na jam'iyyar APC ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Kwali da kuri'u 17,032
- Dan takarar na APC ya doke Haruna Pai na PDP wanda ya samu kuri'u 8,575 a zaben na ranar Asabar da aka gudanar
- Zuwa yanzu jam'iyyar APC ta lashe kananan hukumomi uku da suka hada da AMAC da Bwari da kuma Kwali a zaben Abuja
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta sanar da wanda ya lashe zabe a karamar hukumar Kwali da ke birnin tarayya Abuja.
Daniel Nuhu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen shugabancin ƙaramar hukumar Kwali da ƙuri’u 17,032, a cewar hukumar INEC.

Source: Getty Images
APC ta lashe zabe a karamar hukumar Kwali
Nuhu ya samu nasara ne a mafi yawan mazabu inda ya doke Haruna Pai na jam’iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri’u 8,575 kacal a zaɓen na ranar Asabar inji rahoton Premium Times.
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na INEC ne ya sanar da wannan sakamako a babban ɗakin tattara sakamako na Kwali a safiyar ranar Lahadi yanzu.
Sakamakon zaɓen Kwali ya nuna: Daniel Nuhu na APC ya samu 17,032, yayin da Haruna Pai na PDP ya samu 8,575, wanda hakan ya ba APC damar yin nasara.
APC ta lashe kananan hukumomi 3 a Abuja
Wannan nasara a Kwali na nufin cewa jam’iyyar APC ta lashe zaben ƙananan hukumomi uku cikin huɗu da aka sanar da sakamakon su zuwa yanzu.
Baya ga Kwali, APC ta lashe AMAC da Bwari, yayin da jam'iyyar PDP ta samu nasara a Gwagwalada kawai a cikin wannan zaɓe yau.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an gudanar da zaɓen ne a dukkan mazabu guda 10 na ƙaramar hukumar ta Kwali cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata matsala ba.
Ana sa ran sabon shugaban zai mayar da hankali kan ayyukan raya ƙarkara da kuma inganta rayuwar manoma da ke zaune a yankunan Kwali baki ɗaya.

Source: Getty Images
Martanin mazauna Kwali
Mazauna yankin Kwali sun bayyana farin cikinsu da yadda aka gudanar da zaɓen, inda suke fatan ganin sababbin sauye-sauye a ɓangaren ilimi da samar da ruwan sha.
Tun a lokacin yakin neman zabe, Daniel Nuhu ya yi alƙawarin cewa zai tafi da kowa da kowa ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ko ƙabila ba a yanzu.
Legit Hausa ta tattaunawa da Hajiya Maryama Lawal Mailafia, mazauniyar Kwali, inda ta bayyana cewa:
"Muna fatan sabon shugaban karamar hukumar zai cika dukkan alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe.
"Duk da ina dan fama da ciwon kafa, haka na lallaba na je na kada kuri'a ta. Jama'a da dama ba su fito zaben ba, watakila ko don saboda azumi.
"Allah yasa ya zamo shugaba na-gari, wanda zai kawo ci gaba ga wannan karamar hukuma. Amin."
PDP ta lashe zaben ciyaman a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mohammed Kasim na jam'iyyar PDP ya lashe zaben ciyaman na karamar hukumar Gwagwalada da kuri'u 22,165.
Kasim ya samu ƙuri'u 22,165, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Yahaya Shehu, wanda ya samu ƙuri'u 17,788.
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen, Philip Akpen, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana a dukkanin yankunan ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng


