APC Ta Kowa ce: An Zabi Igbo daga Anambra cikin Shugabannin Jam’iyya a Arewa

APC Ta Kowa ce: An Zabi Igbo daga Anambra cikin Shugabannin Jam’iyya a Arewa

  • Wani ɗan asalin Anambra ya zama Mataimakin Sakataren jam'iyyar APC a Gombe ta hanyar yarjejeniya da aka yi
  • Edwin Chukwujekwu ya ce nasararsa ta nuna haɗin kai da adalcin APC, inda ya jaddada cewa ba a ware kowa a cikin jam’iyyar ba
  • Shugaban kwamitin zaɓe, Danjuma Dabo, ya ce zaɓen yarjejeniya na cikin kundin tsarin APC, yana ƙarfafa haɗin kai domin 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bolari, Gombe - Wani ɗan asalin jihar Anambra, Mista Edwin Chukwujekwu, ya samu nasarar zama daya daga cikin shugabannin APC bayan taron jam'iyyar.

An zabi Chukwujekwu a matsayin Mataimakin Sakataren jam’iyyar APC na mazabar Bolari ta Gabas a ƙaramar hukumar Gombe ta jihar Gombe.

Dan Anambra ya samu mukamin jam'iyya a Gombe
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe. Hoto: Muhammadu Inuwa Yahaya.
Source: Twitter

Gombe: An zabi Igbo daga cikin shugabannin APC

Daily Trust ta ruwaito cewa Chukwujekwu tare da sauran mambobin kwamitin zartarwa na mazaba sun samu nasara ne ta hanyar yarjejeniya a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

PDP ko APC?: INEC ta fadi jam'iyyar da ta lashe zaben ciyaman a Bwari, Abuja

Da yake mayar da martani kan nasararsa a wata hira da manema labarai, ya ce zaɓensa “ya nuna balagar dimokuraɗiyyar APC, musamman wajen inganta haɗin kan ƙasa.”

Ya bayyana zaɓensa a matsayin abin ƙarfafawa ga waɗanda ba ’yan asalin jihar ba, yana mai cewa jam’iyyar ta nuna girmamawa ga haɗin kai kuma “ba ta nuna wariya ga mambobinta.”

Ya ce:

“Ina farin ciki da kasancewa cikin shugabannin jam’iyya a matakin ƙasa da ƙasa, zaɓena ya nuna yanayin adalcin jam’iyyar, kuma ina ba ’yan uwana Igbo shawara su shiga siyasar jam’iyyar.
“Ba a ware mu a cikin jam’iyyar ba. An karɓe mu gaba ɗaya. Da aka zaɓe ni, hakan na nufin muna ciki kuma ba a ware mu ta kowace hanya ba.
“Na kwashe shekaru huɗu ina zaune a nan, kuma yanzu an zaɓe ni cikin kwamitin zartarwa na mazabar jam’iyyar.”
An yi babban taron APC a Gombe
Taswirar jihar Gombe da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Shawarar Chukwujekwu ga yan uwansa

Haka kuma, ya shawarci sauran waɗanda ba ’yan asalin jihar ba da su shiga harkokin siyasa, yana mai cewa APC ta jihar Gombe “ta nuna cewa a buɗe take ga dukkan ’yan Najeriya.”

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben 'dan Majalisa da aka gudanar yau Asabar

Chukwujekwu ya yaba wa gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya bisa salon mulkinsa na haɗin kai, wanda ya haifar da naɗa ɗan asalin Igbo a matsayin Mataimaki na Musamman kan Harkokin Hulɗar Al’umma, cewar Peoples Gazette.

Rahotanni sun nuna cewa jerin sunayen shugabannin mazabu daga mazabu 10 na ƙaramar hukumar Gombe an miƙa su ga shugaban kwamitin kula da zaɓen mazabu da ƙaramar hukuma na jihar, Dakta Danjuma Dabo.

Yar majalisa ta sha da kyar a taron APC

Mun ba ku labarin cewa yar majalisar tarayya ta tsallake rijiya da baya yayin da rikici ya barke a taron jam’iyyar APC a Ethiope ta Yamma, Jihar Delta.

Rikicin ya fara ne bayan sauya wurin taron daga Oghara zuwa Ovade, lamarin da ya haddasa tashin hankali da jikkata wasu.

‘Yar tsohon gwamnan Delta, James Onanefe Ibori, ta roki magoya bayanta su kwantar da hankula tare da neman jami’an tsaro su shawo kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.