Hukumar INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben 'Dan Majalisa da Aka Gudanar Yau Asabar
- Hukumar INEC ta kammala tattara sakamakon zaben cike gurbin da aka gudanar a mazabar Ahoada ta Gabas a jihar Ribas
- 'Dan takarar APC, Ukalikpe Napoleon shi ne ya samu nasara da kuri'u 3,980, inda ya lallasa abokan hamayyarsa a zaben da aka gudanar yau Asabar
- Jami'ar INEC, Farfesa Rosemary Ogbo, ce ta sanar da sakamakon tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin tsari, adalci da gaskiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), ta ayyana ɗan takarar APC, Ukalikpe Napoleon, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na mazabar Ahoada ta Gabas a jihar Ribas.
A yau Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026 INEC ta gudanar da zaben dan Majalisa mai wakiltar Ahoada ta Gabas a Majalisar dokokin jihar Ribas.

Source: Facebook
The Nation ta ce jami'ar INEC, Farfesa Rosemary Ogbo, ce ta sanar da sakamakon tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin tsari da adalci.
Sakamakon zaɓen da INEC ta sanar
A cewar Farfesa Ogbo, Ukalikpe ya samu ƙuri’u 3,980, inda ya kayar da babbar abokiyar hamayyarsa, Ego Marvelous ta jam’iyyar AA, wadda ta samu ƙuri’u 33 kacal, in ji Vanguard.
Sauran sakamakon ya nuna cewa:
- Godstime Egor (APN) – ƙuri’u 38
- Oseja Clifford (Boot Party) – ƙuri’u 11
- Ephraim Raphael Ede (NNPP) – ƙuri’u 7
- Ogide Samson Greatman (YPP) – ƙuri’u 7
- Kwodu Saturday Prosper (ZLP) – ƙuri’u 6
Farfesa Ogbo ta bayyana cewa Ukalikpe ya cika dukkan sharuɗɗan doka tare da samun mafi yawan ƙuri’u masu inganci, don haka aka ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.
Martanin wanda ya yi nasara
Tun kafin sanar da sakamakon, Ukalikpe ya yaba wa masu kaɗa ƙuri’a bisa fitowarsu domin sauke haƙƙinsu na zaɓe. Ya yi zaɓensa a mazaba ta 1, Ward 9, a karamar hukumar Ahoada ta Gabas.
Ya ce ya gamsu da yadda zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali da tsaro, yana mai cewa bai fuskanci wata matsala ba yayin tantancewa da kaɗa ƙuri’a.
“Na bi dukkan matakai, na ga sunana cikin tsarin, kuma na kaɗa ƙuri’a ba tare da wata matsala ba. Ina ganin ya kamata ’yan Najeriya su yaba wa Shugaba Bola Tinubu da INEC bisa yadda aka gudanar da zaɓen,” in ji shi.

Source: Facebook
INEC ta cire jam'iyyu 3 a zaben Kano
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ba ta sanya jam'iyyun adawa uku, PDP, NNPP da ADC a zaben cike gurbin da ya gudana a jihar Kano ba.
Rahotanni sun nuna cewa babu tambarin ko daya daga cikin wadannan jam'iyyu a takardar kada kuri'a da aka gani a zaben da ya gudana yau Asabar a Ungogo da Kano Municipal.
Duk da cewa INEC ba ta yi cikakken bayani kan dalilin cire su ba, jam’iyyun da abin ya shafa sun zargi hukumar da hana su amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki.
Asali: Legit.ng

