Yar Majalisar Ta Sha da Kyar da Rikici Ya Barke a Taron APC, 'Yar Tsohon Gwamnan Ta Yi Magana
- Yar majalisar tarayya ta tsallake rijiya da baya yayin da rikici ya barke a taron jam’iyyar APC a Ethiope ta Yamma, Jihar Delta
- Rikicin ya fara ne bayan sauya wurin taron daga Oghara zuwa Ovade, lamarin da ya haddasa tashin hankali da jikkata wasu
- ‘Yar tsohon gwamnan Delta, James Onanefe Ibori, ta roki magoya bayanta su kwantar da hankula tare da neman jami’an tsaro su shawo kan lamarin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ethiope, Delta - ‘Yar tsohon gwamnan Jihar Delta, Erhiatake Ibori-Suenu, ta tsira da ranta bayan wata rigimar jam'iyyar APC a jihar Delta.
Yar majalisar tarayya ta tsira ba tare da jin rauni ba bayan da rikici ya barke a taron jam’iyyar APC a karamar hukumar Ethiope ta Yamma a jihar.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da yar majalisar ta fitar wanda The Guardian ta samu a yau Asabar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.
An samu hatsaniya a taron jam'iyyar APC
A cewar sanarwar, ta ce an fara shirya gudanar da taron ne a filin wasa na Oghara, amma daga bisani aka sauya wurin zuwa Ovade cikin karamar hukumar, matakin da ta ce ya kara haddasa tashin hankali a tsakanin mambobin jam’iyyar.
‘Yar majalisar ta bayyana cewa rikicin ya barke ne jim kadan bayan isowarta sabon wurin taron, inda ta zargi wasu da ake kyautata zaton ‘yan daba ne da kai hari kan mambobin jam’iyyar, lamarin da ya jikkata mutane da dama.
An ce an kai wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka asibiti domin ba su kulawa na musamman yayin da suke jinya, cewar Vanguard.

Source: Original
Zargin da 'yar majalisar tarayya ta yi
Ibori-Suenu ta kuma yi zargin cewa an hana ta shiga harabar taron sakamakon barazanar tsaro da aka samu, sai dai jami’an tsaron da ke tare da ita sun tabbatar da cewa ba a cutar da ita ba.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta
Rahotanni sun ce har yanzu ana fargabar zaman dar-dar a wasu sassan karamar hukumar, inda ta bukaci jami’an tsaro su kara zage damtse domin hana sake barkewar rikici da tabbatar da doka da oda.
Ibori-Suenu, wacce ‘diya ce ga tsohon gwamnan jihar Delta, James Onanefe Ibori, ta roki magoya bayanta su kwantar da hankula tare da kauce wa duk wani abu da zai kara tayar da fitina a yankin.
An rasa rayuwa a taron APC
Kun ji cewa taron zaɓen mazabu na jam’iyyar APC da ke gudana a jihar Ondo ya rikide zuwa tashin hankali, inda mutane biyu suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata.
Lamarin ya faru ne kasa da awa 24 bayan wasu ’yan daba sun kai hari sakatariyar APC da ke Akure, inda suka tarwatsa taron masu ruwa da tsaki da ake tsaka da yi.
Rahotanni sun ce an kai harin ga shugabannin jam'iyyar mai mulki a jihar da sauran jagororin jam’iyyar a jihar, tare da jikkata wasu mambobi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
