Kurunkus: Pantami Ya Wanke Kansa kan Batun 'Haramtawa' Malamai Shiga Siyasa a Baya

Kurunkus: Pantami Ya Wanke Kansa kan Batun 'Haramtawa' Malamai Shiga Siyasa a Baya

  • Shahararren malamin addinin Musulunci kuma tsohon Minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi magana kan wasu abubuwa da ake yadawa a kansa
  • Farfesa Pantami ya warware zare da abawa kan batun cewa ya taba haramtawa malamai shiga siyasa a baya, amma kuma ga shi yanzu ya shiga cikinta
  • Tsohon Ministan na sadarwa ya bayyana cewa shigar mutane masu nagarta zuwa cikin siyasa abu ne wanda ake so

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya kare kansa kan batun ya taba cewa kada malamai su shiga siyasa.

Farfesa Pantami ya bayyana cewa bai taba haramtawa malamai shiga a dama da su cikin harkokin siyasa ba.

Pantami ya yi magana ka shigarsa siyasa
Farfesa Isa Ali Pantami a wajen karatu a masallaci Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Malamin addinin Musuluncin ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da tashar BBC Hausa, wadda aka sanya a Facebook ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya fadi dalilin shiga siyasa da neman gwamna a Gombe

Me Pantami ya ce kan haramta shiga siyasa?

Farfesa Pantami ya bayyana cewa batun hana shiga siyasa bai taba fitowa daga bakinsa, ya kuma kalubalanci duk wanda yake da hujja to ya nuna masa ita.

"Ban taɓa cewa shiga siyasa haramun ba ne, idan akwai wanda ya taɓa ji , ina so ya kawo min wurin."

- Farfesa Isa Ali Pantami

Farfesa Pantami ya bayyana cewa da yawa daga cikin bidiyoyin karatunsa na baya kan siyasa da a yanzu suke yawo a shafukan sada zumunta an sauya su ne.

''Da yawa daga cikin waɗannan bidiyoyin an yayyanke su an jojjona su da juna, galibi ba a kan maudu'in da ake magana na yi su ba. Don haka ni ban taba haramta shiga siyasa ba."

- Farfesa Isa Ali Pantami

Pantami ya yi magana shiga siyasa

Farfesa Pantami ya bayyana cewa manyan malamai masu nagarta a ciki da wajen Najeriya sun yi kira ga mutane masu nagarta su shiga cikin harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya da sojojin Ukraine suka cafke a yaki da Rasha ya roki Tinubu alfarma

''Ina da sautin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, da Sheikh Dahiru Bauchi da Dr Bashir Aliyu Umar da Dr Sani Umar Rijiyar Lemo da wasu da dama na kiran cewa ya kamata mutane masu nagarta su shiga siyasa."

- Farfesa Isa Ali Pantami

Ya kawo maganganu malamai

Tsohon Ministan ya bayyana cewa yana da fatawoyin manyan malaman duniya da suka ce a shiga siyasa.

Farfesa Pantami ya sabunta rajistarsa da APC
Farfesa Isa Ali Pantami a wajen sabunta rajistarsa ta jam'iyyar APC Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook
''Ina da manyan fatawar malaman duk duniya ba na Najeriya ba, irin Ibn Usaymin da ke cewa shigar ma wajibi ne. Dokta Bashir da ya zo ya cr mutane masu tarbiyyar addini su shiga wajibi ne."
"To gaya mini wani malami mai daraja da ya fi wadannan da ya fito ya ce kar a shiga. Duk inda ka ga wani ya kalubalanci shigar wani, to wanda ya shigar matsala ne ga mai gidan wancan da ke maganar. Inda ba matsala ba ne ba ruwansa."
"Ai ba yanzu masu addini suna fara yi ba. Ai a Kano an yi babban shehi wanda ya tsaya takarar gwamna ba daya ba, ba biyu ba. A nan jihar Neja, an yi babban shehi ya tsaya takara."
"Amma me yasa na mu ya tsole ido, saboda tasirin shigar ake tsoro, kuma duk wanda yake magana yana kara mana karfin mu shiga ne. Idan da tsammanin shigar dari bisa dari ne, to yanzu ya koma miliyan bisa miliyan."

Kara karanta wannan

Bincike ya tono yadda tsohon ministan Najeriya ya sharara karya a gaban duniya

- Farfesa Isa Ali Pantami

'Yar siyasa ta ragargaji Pantami

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitacciyar 'yar siyasa, Hajiya Najaatu Muhammad, ta ragargaji tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.

Hajiya Naja'atu ta bayyana Farfesa Pantami a matsayin makaryaci kan maganganun da ya rika yi kan siyasa a baya.

Ta bayyana cewa Pantami ya na kuka, yana la'antar siyasa, yana tir da karbar mulki amma a karshe ya zo ya karbi mukamin minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng