Shugabannin APC Sun Kai Wa Gwamna Ziyara, Ana Rade Radin Zai Canza Jam'iyya
- Shugabannin jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa sun kai ziyarar ban girma ga Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a gidan gwamnati da ke birnin Yola
- Wannan ziyara da aka kai yau Juma'a, 20 ga watan Fabrairu, 2026 na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin gwamnan zai bar PDP ya koma APC
- Majiyoyi daga fadar gwamnatin jihar Adamawa sun nuna cewa jiga-jigan sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi shugabanci da siyasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa, Nigeria - Alamu na kara karfi tare da nuna cewa watakila nan ba da jimawa ba jam'iyyar APC za ta karbi gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri.
Rahotannin da muka samu sun nuna cewa shugabannin jam'iyyar APC sun kai ziyarar ban girma ga Gwamna Ahmadu Fintiri a gidan gwamnatinsa da ke birnin Yola yau Juma'a.

Kara karanta wannan
Gwamnan Taraba ya karbi makudan kudade kafin ya sauya sheka zuwa APC? Gaskiya ta fito

Source: Original
Jiga-jigan APC sun kai ziyara ga Gwamna Fintiri
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa jiga-jigan jam'iyyar APC sun ziyarci gwamna Fintiri ne a daidai lokacin da ake rade-radin yana shirin dauya sheka daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki a kasar nan.
Tawagar jiga-jigan siyasar ta samu jagoranci daga Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, inda suka kai ziyarar ta musamman a Gidan Gwamnati da ke Yola.
Ana rade-radin Gwamnan Adamawa zai koma APC
Majiyoyi daga gidan gwamnatin sun bayyana cewa manufar ziyarar ita ce ƙarfafa tattaunawa, inganta haɗin kai da kuma bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin shugabannin siyasa domin ci gaban Jihar Adamawa.
Bugu da kari, wasu majiyoyi sun ce ganawar ta yi nazari tare da duba yiwuwar sauya sheƙar Gwamna Fintiri zuwa jam'iyyar APC gabanin taron zaɓen shugabannin jam’iyya.
Abin da jiga-jigan APC suka tattauna da Fintiri
A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun tattauna kan muhimman kalubale na ci gaba da ke fuskantar jihar, tare da duba hanyoyin da za a ƙarfafa haɗin gwiwa domin amfanin al’ummar Adamawa.
Shugabannin jam’iyyar APC sun jaddada cewa gina shugabanci a kan tubalin tattaunawa da fahimtar juna yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Source: Twitter
Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta hasashen yiwuwar sauya sheƙar Gwamna Fintiri, lamarin da zai iya sauya yanayin siyasar Adamawa a nan gaba.
Gwamna Fintiri ya dauki zafi kan ihun matasa
A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasa sun fusata Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a Ganye, Adamawa, yayin taron neman goyon bayan jam'iyyar PDP.
Rahoto ya nuna cewa matasan sun rika ihu suna cewa 'ba mu yi, ba mu yi...' lamarin da ya fusata Gwamna Fintiri har ya ya dakata kuma ya mayar masu da martani cikin fushi.
Gwamna Fintiri ya kalubalanci masu adawa da shi kan zabe, yana mai cewa su tsayar da dan takara, shi ma ya tsayar, a ga wanda zai ci zabe
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
