ADC, Kungiyoyi Sun Nuna Damuwa kan Gaggawar Tinubu na Amincewa da Dokar Zabe
- Kungiyoyin farar hula sun soki rattaba hannu kan Dokar Zabe ta 2026 da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi
- Sun bayyana cewa gaggawar da majalisun kasar nan suka yi wajen amincewa da dokar, da sa hannun Tinubu abin a duba ne
- A gefe guda kuma jam'iyyar adawa ta ADC ta bayyana yadda gaggawar amincewa da dokar zai jawo matsala a zaben 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam'iyyar adawa ta ADC, Cibiyar Kukah Centre da Yiaga Africa tare da wasu kungiyoyin farar hula sun caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sun bayyana damuwa a kan yadda ya yi gaggawar rattaba hannu a kan Dokar Zabe ta 2026, a ranar Alhams, 19 ga watan Fabrairu, 2026.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa kungiyoyin sun bayyana matsayinsu ne a wani taron manema labarai a Abuja karkashin hadakar kungiyoyi.
Kungiyoyi sun dura a kan Tinubu
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa daga ciki kungiyoyin da suka shirya taron akwai International Press Centre, TAF Africa, Centre for Media and Society, Nigerian Women Trust Fund da Elect Her.
Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin ne a Fadar Shugaban Kasa bayan majalisun biyu na wakilai da na dattawa sun amince da shi, duk da ce-ce-ku-ce kan wajabcin tura sakamakon zabe ta na’ura kai tsaye shafin INEC.
Jake Epelle na TAF Africa ya ce saurin da aka yi wajen zartar da dokar da kuma rashin cikakken bayani ya taba yardar da jama’a suke da shi a kan dokar.
Ya kara da cewa amincewa da kudirin ba tare da warware muhimman matsalolin doka da fasaha ba na iya rage kwarin gwiwar jama’a ga tsarin zabe.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta
Kungiyoyin sun kuma soki sanya harajin Naira miliyan 50 domin rajistar sabuwar jam’iyya, suna cewa hakan zai hana matasa da kungiyoyin jama'a shiga takara.
Haka kuma sun ce takaita zabin fidda gwani zuwa zaben kai tsaye ko yarjejeniya na iya kara hadarin sayen kuri’u.
ADC ta caccaki Tinubu kan dokar zabe
Jam’iyyar hamayya ta ADC ta zargi Shugaba Tinubu da raunana sahihancin zabe, tana mai cewa za ta hada kan ‘yan Najeriya domin kare kuri’unsu ta hanyoyin doka.

Source: Facebook
A gefe guda, kungiyar ACF ta goyi bayan sa hannun cikin gaggawa, tana cewa lokaci na kurewa kafin zaben 2027.
Sai dai ta bukaci a fitar da cikakken bayanin dokar domin jama’a su fahimci dukkannin tanade-tanaden da ke kunshe a cikinta.
Yayin da ake ci gaba da buga muhawara a kan batun, kungiyoyin farar hula sun ce za su ci gaba da sa ido kan yadda za a aiwatar da dokar kafin babban zabe mai zuwa.
Kwankwasiyya ta soki Tinubu
A baya, kun samu labarin cewa
Asali: Legit.ng
