Gwamna Ya Fusata da Rigimar APC Ta Lakume Rayukan Mutane 2, Ya ba da Umarni
- Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya umarci jami’an tsaro su binciki rikicin taron APC na mazabu da aka yi a jihar
- ‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum biyu, yayin da uku suka jikkata a rikicin wanda ake zargin yan daba
- Jam’iyyar APC ta jihar ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin tare da hukunta masu hannu a ciki domin zama izina ga saura
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ondo - Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya fusata bayan mummunan rigima da ta barke a taron APC.
Gwamna Aiyedatiwa ya ba hukumomin tsaro umarnin su gano tare da gurfanar da wadanda ke da alhakin rikicin da ya tarwatsa taron mazabu na jam’iyyar.

Source: Facebook
An gudanar da taron mazabu a dukkan mazabu 203 na jihar, amma rikici ya barke a wasu sassan Karamar Hukumar Idanre, cewar The Nation.
Yadda rigimar APC ta lakume rayuwa
Ana zargin wasu matasa ‘yan daba masu alaka da ‘yan kungiyar sufuri sun kawo cikas ga taron wanda ya jawo asarar rayuka.
Rahotanni sun ce rikicin ya bazu zuwa wasu yankuna da ke wajen babban birnin jihar, musamman a Iju/Ita-Ogbolu da ke Karamar Hukumar Akure ta Arewa, inda aka samu fada da tashin hankali na tsawon sa’o’i.
‘Yan sanda sun tabbatar da cewa mutum biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu uku suka samu raunuka sakamakon hare-haren.
Daya daga cikin wadanda abin ya shafa shi ne Mista Raphael Adetimehin, kanin shugaban APC na jihar, Injiniya Ade Adetimehin, wanda ake zargin an yi masa mugun duka kuma yana kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.

Source: Twitter
Sanarwar da Gwamna Aiyedatiwa ya fitar
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Prince Ebenezer Adeniyan, ya fitar, gwamnan ya yi Allah-wadai da tashin hankalin, yana mai cewa ba shi da alaka da lamarin.
Ya kuma umurci jami’an tsaro da su dawo da zaman lafiya tare da gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta masu hannu a rikicin, cewar The Guardian.
Sanarwar ta kuma yi kira ga duk masu neman mukamai a jam’iyyar da su ja kunnen magoya bayansu, tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani karya doka da oda ba.
Ya ce:
“Mai girma Gwamna ya kira yi hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan rikicin da ya faru a Idanre a yau, tare da kamo wadanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci.”
Haka zalika, shugabanni da dattawan jam’iyyar karkashin 'PBAT Mandate Elders Forum' sun yi Allah-wadai da rikicin, inda suka bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ba da umarnin gudanar da bincike kan tashin hankalin da ya auku a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Yan daba sun raunata shugaban APC a Ondo
Kun ji cewa wasu da ake zargin mambobin kungiyar NURTW ne sun kai hari sakatariyar APC inda aka raunata wasu manyan mutane a ofishin.
Shugaban APC na jihar, Ade Adetimehin, ya ce an jefa shi ƙasa tare da yi masa dukan tsiya yayin rikicin da ya barke kan taron siyasa.
An zargi magoya bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ɗaukar nauyin harin, amma ɓangaren gwamnan bai mayar da martani ba.
Asali: Legit.ng

