Ana cikin Azumi, Sanata Rufai Hanga Ya Burma Matsala a Kotun Musulunci a Kano
- An maka Sanata Rufa'i Hanga a gaban kotun shari'ar Musulunci da ke Shahuci a cikin birnin Kano kan zargin kin biyan hakkokin yakin neman zaben 2023
- Masu kara sun gabatar da hujjoji a gaban kotu, inda suka nemi Sanata Hanga, mai wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa ya biya su N124,800,070
- Da aka zauna a kotu, lauyan Sanata Hanga ya roki kotu da ta yi watsi da karar gaba daya amma Mai Shari'a Muhammad Sani ya ki amincewa da hakan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Babbar Kotun Shari’a da ke Shahuci a Kano, ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan Sanata Rufai Sani Hanga, mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Shari’ar ta shafi zargin Sanata Rufai Hanga da rashin biyan kuɗin ayyukan kamfen da suka kai kusan N124,800,070.

Kara karanta wannan
"Ana buƙatar taimako": Shehu Sani ya yi maraba da girke sojojin Amurka a Najeriya

Source: Twitter
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa an shigar da wannan kara ne gaban Mai Shari'a Muhammad Sani na kotun shari'ar musulunci.
Abin da masu ƙarar Rufai Hanga ke zargi
Isa Ado Medoya da wasu mutane sun shigar da ƙara bisa zargin cewa sun yi wa Rufa'i Hangankamfen kamar yadda doka ta amince a lokacin zaɓen sanatan, amma har yanzu ba a biya su haƙƙinsu ba.
Alƙali Muhammad Sani ya buɗe zaman kotun inda lauyan masu ƙara ya gabatar da hujjojin da gabatar da karar. A cewar masu ƙara, kuɗin da suke nema diyya ne kan ayyukan da suka yi a lokacin kamfen.
An fara gabatar da hujjoji kan Sanata Hanga
Lauyan masu ƙara, Barrista Abbas Sani Abubakar Mandawari, ya gabatar da wasu takardu da hujjoji da nufin nuna yadda aka gudanar da aikin.
Sai dai ya sanar da kotu cewa yana buƙatar ƙarin lokaci domin tuntuɓar wadanda yake karewa da tsara wasu takardu da suka rage, tare da neman a ba su lokaci domin tabbatar da wasu bayanai.
Martanin ɓangaren Sanata Rufa'i Hanga
Lauyan wanda ake ƙara ya yi fatali buƙatar, yana mai cewa alamar rashin shiri ce daga ɓangaren masu ƙara.
Ya roƙi kotu ta yi watsi da ƙarar, yana mai cewa jinkirin ya nuna ba su shirya bin shari’ar yadda ya kamata ba, in ji rahoton Daily Post.
Sai dai kotun ta ƙi amincewa da roƙon yin watsi da ƙarar, inda ta yanke hukuncin bai wa masu ƙara ƙarin lokaci domin su karisa gabatar da takardunsu.

Source: Facebook
Kotun musulunci ta ɗage zaman shari’ar
Alƙalin ya jaddada muhimmancin bai wa kowane ɓangare cikakkiyar dama domin gabatar da hujjoji da bayanansa yadda ya kamata.
An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026, inda ake sa ran masu ƙara za su gabatar da cikakkun takardu, sannan lauyan wanda ake ƙara zai miƙa martaninsa a hukumance.
Sanata Kawu ya dura kan Ado Doguwa
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Kawu Sumaila ya roki jama’a su guji mayar wa Alhassan Ado Doguwa martani, yana cewa yana fuskantar wata matsala.
Kawu Sumaila ya yi martanin ne bayan mutane suna ta kiransa kan lamarin Hon. Doguwa saboda maganganu da ya yi a wani taron APC a Kano.
'Dan majalisar kudancin Kano ya ce Alhassan Doguwa ba zai fahimci yana cikin wani hali ba saboda haka lalurar take, inda ya ce addu'a da hakuri yake bukata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

