Zance Ya Kare, Majalisar Dokoki Ta Canza Shawara kan Shirin Tsige Gwamna Fubara

Zance Ya Kare, Majalisar Dokoki Ta Canza Shawara kan Shirin Tsige Gwamna Fubara

  • Majalisar dokokin jihar Ribas ta janye shirinta na sauke Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu daga kan mulki
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani domin sulhunta rikicin siyaar jihar Ribas
  • A zamansu na yau Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026, yan Majalisar sun gabatar da kudirin dakatar da shirin tsige gwamnan kuma an amince da shi nan take

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta dakatar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

Ana ganin dai Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani tare da sulhuna Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Fubara.

Gwamna Fubara.
Gwamna Siminalayi Fubara a gidan gwamnatin Ribas da ke birnin Fatakwal Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an yanke shawarar janye shirin tsige gwamnan ne a ranar Alhamis yayin zaman majalisar dokokin a birnin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

An ji abin da ya roka da Tinubu ya yi waya da Shugaban gwamnatin kasar Jamus a tarho

Rahotanni sun nuna cewa a zaman, ’yan majalisar sun gabatar da kudurin dakatar da shirin tsige gwamnan, kuma aka amince da shi nan take.

Zarge-zargen da majalisa ta yiwa Fubara

Tun da farko, majalisar ta fara shirin tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa a zaman farko na shekarar 2026, bisa zargin aikata manyan laifuffuka da suka karya kundin tsarin mulki.

Daga cikin mambobi 32 na Majalisar, 26 sun sanya hannu kan takardar yin amfani da Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka gyara) don cire gwamnan da mataimakinsa

Laifuffukan da aka zargi gwamnan da aikatawa sun hada da rushe ginin Majalisar Dokokin Jihar, amincewa da kashe kuɗaɗe ba tare da sahalewar majalisa ba da sauran zarge-zarge makamantansu.

Yadda Bola Tinubu ya sulhunta Wike da Fubara

Dakatar da shirin tsigen na zuwa ne bayan shiga tsakani da aka ce Shugaba Tinubu ya yi domin daidaita rikicin siyasa da ke faruwa a jihar.

Tribune Nigeria ta tattaro cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Ribas, Sim Fubara da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta ji koken musulmai, ta gyara dokar zabe saboda azumin Ramadan

An yi ganawar ne a gidan Shugaba Tinubu da ke fadar shugaban kasa, kuma wasu bayanai sun nuna cewa Gwamna Fubara ya duka ya roki Wike ya yafe masa.

Kakakin Majalisar dokokin Ribas.
Shugaban Majalisar dokokin jihar Ribas, Rt. Hon. Martins Amaewhule Hoto: Rivers State House of Assembly
Source: Facebook

Taron da aka yi kwanan nan da Ministan Babban Birnin Tarayya da Gwamna Fubara shi ne karo na biyu da Tinubu ya shiga tsakani kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin su biyun.

Gwamna Fubara ya rusa Majalisar zartarwa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Ribas, Sir Siminalayi Fubara, ya sanar da korar dukkan kwamishinoni da sauran mambobin majalisar dokokin jihar.

Matakin rushe majalisar ya zo ne sa’o’i 48 bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike , ya tabbatar da cewa ana kokarin sasanta rikicin siyasa da ya dade yana faruwa a jihar.

Gwamna Fubara ya umarci dukkan kwamishinoni da masu ba shi shawara namusamman da su mika ragamar aiki nan take, tare da gode masu bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262