Gwamnan Taraba Ya Karbi Makudan Kudade kafin Ya Sauya Sheka zuwa APC? Gaskiya Ta Fito

Gwamnan Taraba Ya Karbi Makudan Kudade kafin Ya Sauya Sheka zuwa APC? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya karyata labarin da ke yawo cewa an ba shi makudan kudi kafin ya sauya zuwa APC
  • Gwamna Kefas ya nuna kwarin gwiwa cewa zai iya kawo wa Shugaba Tinubu nasara a Jihar Taraba a zaɓen 2027
  • Ya ƙaryata jita-jitar cewa akwai saɓani tsakaninsa da dattijon ƙasa kuma tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Danjuma (mai ritaya)

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba, Nigeria - Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya musanta zargin cewa ya karbi makudan kudi daga gwamnatin tarayya kafin ya amince ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Gwamna Kefas ya ce labarin da ake yadawa cwwa gwamnonin da suka fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC sun karɓi kuɗi kafin sauya sheƙarsu, ba gaskiya ba ne.

Gwamna Agbu Kefas.
Gwannan jihar Taraba, Agbu Kefas yana jawabi a taro a fadar gwamnatinsa Hoto: Agbu Kefas
Source: Facebook

Haka kuma, gwamnan ya ƙaryata jita-jitar cewa akwai saɓani tsakaninsa da dattijon ƙasa kuma tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Danjuma (mai ritaya), kamar yadda Vangaurd ta kawo.

Kara karanta wannan

Dauda Lawal: Gwamnatin Tinubu ta mayar da Zamfara saniyar ware saboda muna PDP

Kefas ya yi wannan bayani ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Gwamna Kefas ya karbi kudi kafin shiga APC?

“Babu wanda ya ba ni kuɗi domin in koma APC,” in ji shi, yana mai cewa shawarar ta samo asali ne daga akida da kuma la’akari da ci gaban Jihar Taraba, ba wai don wata fa’ida ta kuɗi ba.

Ya kuma bayyana gamsuwarsa da sabon dandalin siyasar da ya koma, yana mai cewa yana da kwarin gwiwa kan damar da APC za ta bai wa jihar

Gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa zai iya kawo wa Shugaba Tinubu nasara a Jihar Taraba a zaɓen 2027, yana mai cewa manufofinsa sun fara yin tasiri a matakin ƙasa.

Gwamnan Taraba ya yi rikici da T.Y Danjuma?

Dangane da jita-jitar cewa yana da matsala da Janar Danjuma, Kefas ya ce babu wata matsala ko rashin jituwa a tsakaninsu.

Ya bayyana Danjuma a matsayin uba a gare shi, yana mai cewa dangantakarsu ta dade kuma ta samo asali tun daga zamaninsu na aikin soja, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fada da ya koma APC

“Ba ni da wata matsala da TY Danjuma; shi ubana ne. Tun da muka fara siyasa babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaninmu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa kafin sauya sheƙarsa, ya sanar da Danjuma kuma ya samu amincewarsa, duk da cewa tsohon janar ɗin ba mamba ba ne a kowace jam’iyya.

Gwamna Agbu Kefas.
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas da tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: Agbu Kefas
Source: Facebook

Bola Tinubu ya yabi gwamnan Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yabawa matakin da gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya dauka na sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Shugaba Tinubu ya bayyana aniyarsa ta ba wa gwamna Kefas da majalisar zartarwarsa cikakken goyon baya domin kawo cigaba a jihar Taraba.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnonin da ke karkashin inuwar jam’iyyar APC su ne jagororin jam’iyyar a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262