‘Renewed Hope’: Tinubu Ya ba Gwamna Uba Sani Shirgegen Mukami gabanin Zaben 2027

‘Renewed Hope’: Tinubu Ya ba Gwamna Uba Sani Shirgegen Mukami gabanin Zaben 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Gwamna Uba Sani a matsayin mataimakin darakta janar na wayar da kan jama'a domin tunkarar zaben 2027
  • Sanarwar nada Uba Sani ta fito ne ta hannun Bayo Onanuga inda ya bayyana cewa gwamnan zai taimaka wajen tallata nasarorin gwamnatin Tinubu
  • Wannan nadin ya biyo bayan fitar da jadawalin zabe daga hukumar INEC wanda ya nuna cewa za a fara yakin neman zabe a Nuwamba, 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, muhimmin nadi yayin da ake tunkarar zabukan shekarar 2027.

A ranar Talata, Tinubu ya nada Uba Sani jakadan "Renewed Hope" kuma mataimakin darakta-janar na hulɗa da jama'a da wayar da kai na jam'iyyar APC.

Shugaba Bola Tinubu ya nada Uba Sani a matsayin jakadan Renewed Hope
Gwamna Uba Sani (hagu) ya kai ziyara ga Shugaba Bola Tinubu (dama) a fadar Aso Rock, Abuja. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Tinubu ya ba Gwamna Uba Sani mukami

Kara karanta wannan

Gobarar Singer: An gano biliyoyin Naira da Tinubu, gwamnonin APC suka ba Kano

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya sanar da wannan nadin a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a yammacin 17 ga Fabrairu, 2026.

Wannan naɗi yana zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaɓen 2027, wanda ya nuna za a fara yakin neman zaben a watan Nuwamba 2026.

Onanuga ya ce Tinubu, a matsayinsa na jagoran jam’iyyar APC, ya naɗa Uba Sani ne saboda “hazakarsa ta shugabanci da kuma bajintarsa wajen tsara ayyuka yadda ya kamata.”

A cewar sanarwar, nauyin da ke kansa ya haɗa da yin aiki kafa-da-kafa da darakta-janar na Jakadun "Renewed Hope" da kuma shugabannin jam’iyya, musamman shugaban APC na ƙasa.

Aikin da ke gaban Gwamna Uba Sani

A cikin sanarwar, Bayo Onanuga ya ce:

"Wannan naɗin na da nufin tabbatar da haɗin kai, tafiye tare da kowa, da kuma tsara dabarun haɗin gwiwa a dukkan matakai na wayar da kan jama'ar Najeriya."

Shugaban Ƙasar ya ce yana sa ran mataimakin darakta-janar ɗin zai “zabura, ya yaɗa shirye-shirye da manufofin jam’iyya, gami da nasarorin da aka samu, domin ƙarfafa amincewar jama’a.”

Kara karanta wannan

Kurunkus: Gwamna Abba ya bayyana ainihin dalilinsa na komawa APC a gaban Shettima

A cikin wasiƙar, Onanuga ya ce babbar manufar Tinubu ta yin nadin ita ce tabbatar da cewa daukacin ƴan ƙasa sun san manufofin jam'iyyar APC tare da goya mata baya a 2027.

Gwamna Uba Sani zai jagoranci wayar da kan jama'a game da ayyukan gwamnatin Tinubu gabanin 2027.
Shugaba Bola Tinubu lokacin da ya karbi bakuncin Gwamnan Kaduna, Uba Sani a fadar Aso Rock. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Manufar nadin jakadan Renewed Hope

Mai magana da yawun shugaban kasar, ya yi bayani cewa an nada jakadan Renewed Hope don tabbatar da cewa daukacin jama'a sun fahimci ayyukan gwamnatin Tinubu, sannan daga ƙarshe su goyi bayan APC da 'yan takarartaa a kowane mataki a zaɓen 2027.

Shugaba Bola Tinubu ya shaidawa Uba Sani cewa:

"Shiri tun da wuri yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma wannan sakamako, kuma shugabancinka zai kasance ginshiƙi wajen jagorantar wannan tsari cikin inganci da dabarun siyasa."

Ana dai kallon wannan mataki a matsayin wani ɓangare na dabarun Shugaba Tinubu na ƙarfafa jiga-jigan jam'iyyar APC daga yankin Arewa domin tunkarar zaɓen da ke tafe.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Tinubu ya sanya labule da Uba Sani

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya gana da Gwamna Uba Sani a fadar Aso Rock bayan sun halarci daurin auren 'ya'yan ministan tsaro.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fada da ya koma APC

Ganawar tasu ta zo ne awanni bayan wasu masu ibada da aka sace a Kaduna sun shaki iskar 'yanci daga hannun azzaluman yan bindiga.

Wannan ziyara ta dauki hankalin 'yan Najeriya saboda yadda shugaban kasar ya dawo ya zauna kan kujerar baki, abin da ba a saba ganin ya yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com