Yan Daba Sun Fasa Ofishin APC, Sun Raunata Shugaban Jam'iyya, Tsohon Dan Majalisa
- Wasu da ake zargin mambobin kungiyar NURTW ne sun kai hari sakatariyar APC inda aka raunata wasu manyan mutane a ofishin
- Shugaban APC na jihar, Ade Adetimehin, ya ce an jefa shi ƙasa tare da dukan tsiya yayin rikicin da ya barke kan taron siyasa
- An zargi magoya bayan gwamna Lucky Aiyedatiwa da ɗaukar nauyin harin, amma ɓangaren gwamnan bai mayar da martani ba.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ondo - Wasu ’yan daba da ake zargin mambobin ƙungiyar NURTW ne sun kai farmaki sakatariyar jam’iyyar APC.
Majiyoyi suka ce matasan sun kai harin ne a jihar Ondo a ranar Talata 17 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.

Source: Twitter
An raunata shugaban APC a Ondo
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban APC na jihar, Injiniya Ade Adetimehin, tare da wasu jami’an jam’iyya sun samu raunuka sakamakon rikicin, cewar Daily Trust.
Cikin waɗanda suka jikkata har da wakilin jihar a hukumar NDDC, Hon. Otito Atikase, tsohon ɗan majalisa, Hon. Success Torhukerhojo, tsohon mataimakin kakakin majalisa, Hon. Abayomi Akinruntan da wasu da dama.
An ce rikicin ya fara ne lokacin da ’yan daban suka kutsa cikin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, lamarin da ya sa mahalarta suka watse cikin firgici tare da dakatar da taron.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shigo da sanduna da adduna, suna ihu tare da barazana ga mahalarta taron.
Wasu daga cikin mahalarta sun tsere zuwa gine-ginen da ke kusa, yayin da wasu motocin suka fice da sauri domin kauce wa tashin hankalin.

Source: Original
Martanin shugaban APC a Ondo
Da yake mayar da martani, Adetimehin ya ce an shirya taron ne domin tanadin gangamin zaɓen gunduma da zai fara a ranar Laraba 18 ga watan Fabrairun 2026.
Ya ce an jefa shi ƙasa tare da yi masa dukan tsiya, inda aka kwace wayoyinsa guda biyu da agogonsa na hannu.
Ya ce:
“Sun zo da ƙarfi a safiyar yau suka umarci kowa ya fita. Sun ce gwamna ne mai jam’iyyar. Mun gaya musu cewa ba mu ƙalubalantar ikon kowa ba, amma sai suka far mana. Sun jefa ni ƙasa, ban damu ba, suka kwace wayoyina guda biyu daga aljihuna tare da agogon hannuna.”
A cewarsa, maharan sun yi iƙirarin cewa gwamnan jihar ne ke da ikon jam’iyyar, kuma ba sa son a gudanar da zaɓen gangami a jihar, cewar The Guardian.
Tsofaffin kwamishinoni da suka tsere daga wurin sun zargi shugaban NURTW na jihar da jagorantar harin tare da zargin cewa an ɗauki nauyin lamarin daga ɓangaren gwamna.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ɓangaren gwamnan bai fitar da wata sanarwa ba dangane da zargin da ake masa.
Hadiman Gwamna sun ajiye aikinsu a Ondo
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Ondo, Lukcy Orimisan Aiyedatiwa, ya rasa wasu daga cikin hadimansa a sakamakon yin murabus daga mukamansu.
Hadiman na gwamnan sun yi murabus ne daga mukamansu a cikin wasikun da suka aika na ajiye aiki a karkashin gwamnatin jihar Ondo.
Daya daga cikin hadiman ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yin aiki a karkashin gwamnatin da Lucky Aiyedatiwa ke jagoranta.
Asali: Legit.ng

