PDP Ta Yi Rashi, Wani Ɗan Majalisa da Magoya bayansa Sun Koma Jam'iyyar APC

PDP Ta Yi Rashi, Wani Ɗan Majalisa da Magoya bayansa Sun Koma Jam'iyyar APC

  • 'Dan majalisar jihar Abia Uchenna Erondu Jnr ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC tare da magoya baya sama da 5,000
  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia Chris Akomas ne ya karbi dan majalisar inda ya bayyana shi a matsayin kadara ga APC
  • A taron sauya sheka, Erondu Jnr ya ce dole ne 'yan kasar su fito su sake zabar Shugaba Bola Tinubu saboda ayyukan da ya shimfida

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abia - A yammacin Talata, dan majalisa mai wakiltar mazaɓar Obingwa-Yamma a majalisar dokokin Abia, Uchenna Erondu Jnr, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Tsohon mataimakin gwamna Chris Akomas ne ya karɓi Erondu Jnr, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ma’aikata a garin Nenu, Obingwa, tare da magoya baya sama da 5,000.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Gwamna Abba ya bayyana ainihin dalilinsa na komawa APC a gaban Shettima

Dan majalisar Abia, Uchenna Erondu Jnr ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Dan majalisar Abia, Uchenna Erondu Jnr (tsakiya) yana daga tsintsiya da ya bar PDP zuwa APC. Hoto: @RealAdvocate27
Source: Twitter

'Dan majalisa ya fice daga PDP zuwa APC

Yayin da yake bayyana dalilinsa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar ta Obingwa ya ce komawa APC zai ba shi damar jawo babban ci gaba ga Obingwa, Abia ta Kudu, da ma jihar baki ɗaya, in ji rahoton Punch

A taron sauya shekar, Uchenna Erondu Jnr ya ce:

“Idan har zan iya cimma abubuwan da na yi lokacin ina PDP, ina tabbatar wa mutanenmu cewa a karkashin jam'iyyar APC, za mu yi fiye da haka."

Ya bayyana goyon bayansa ɗari bisa ɗari ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027, inda ya bayyana cewa manufofin Tinubu sun kawo ci gaba ga Najeriya.

Erondu Jnr ya ƙara da cewa batun sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027 "ba abin a yi wa tantama ba ne" duba da irin sauye sauyen da yake yi wa tattalin arzikin ƙasa.

Wadanda suka jawo dan majalisa APC

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fada da ya koma APC

Sauya sheƙar ta biyo bayan lallashi da manyan jiga-jigan APC suka yi masa, ciki har da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Okezie Kalu, da Uche Nwosu, da Chris Nkwonta.

An ce mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya gana da Erondu Jnr a daren ranar Asabar, inda ya gayyaci ɗan majalisar jihar da ya shigo cikin jam’iyyar APC.

A wajen taron, Dr. Chris Akomas ya ce:

“Erondu Jnr wata kadara ce mai daraja ta fuskar siyasa kuma tsohon mamba ne na asali a APC a jihar Abia.”

Ya gode masa bisa amsa kiran gaggawa na shiga APC, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa dawowar tasa za ta ƙarfafa tsarin jam'iyyar gabanin babban zaɓen 2027.

Ana ganin sauya shekar dan majalisar ta rage tasirin PDP a Abia.
Taswirar jihar Abia, inda wani dan majalisa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tasirin sauya sheƙar dan majalisar

Erondu Jnr ya sauya sheƙar ne tare da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Obingwa, Hon. George Ubani, da Hon. Chikezirim Monday Orji, da kuma magoya baya sama da 5,000.

Sauran manyan jiga-jigan APC da suka halarci taron sun haɗa da Chief Sam Nkire, da tsohon Kakakin Majalisar Abia, Rt. Hon. Christopher Enweremadu, da sauran jami'ai.

Wannan sauya sheƙa babban rashi ne ga PDP a jihar, kodayake ba a samu jin ta bakin shugaban jam'iyyar, Elder Abraham Amah ba, don jin martaninsa.

Kara karanta wannan

Shettima ya fadi muhimmancin Kano ga APC bayan karbar Gwamna Abba zuwa jam'iyyar

Masu lura da lamuran siyasa sun bayyana cewa wannan matakin zai ƙara wa jam'iyyar APC tasiri a yankin Abia ta Kudu, wanda a dā ya kasance karkashin ikon PDP.

Dan majalisar Abia ya fice daga APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, APC ta rasa dan Majalisa daya tilo da take da shi a Majalisar Dokokin Jihar Abia, Hon. Akaliro Kelechi Anderson.

'Dan Majalisar ya tabbatar da sauya sheka daga APC zuwa LP a wata wasika da ya aika wa shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Umuahia ta Arewa.

Ya bayyana cewa ya dade yana nazari kan salon mulkin Gwamna Alex Otti, wanda kuma ya gano cewa mutum ne mai son ci gaban Abia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com