Kurunkus: Gwamna Abba Ya Bayyana Ainihin Dalilinsa Na Komawa APC a gaban Shettima

Kurunkus: Gwamna Abba Ya Bayyana Ainihin Dalilinsa Na Komawa APC a gaban Shettima

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ya fice daga NNPP
  • Abba Kabir Yusuf ya yi bayani a bainar jama'a kan dalilin da ya sanya ya yanke shawarar komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Taron karbar gwamnan na Kano zuwa APC ya samu halartar manyan baki ciki har da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan matakin da ya dauka na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Gwamna Abba ya bayyana cewa shawararsa ta komawa jam’iyyar APC ta samo asali ne daga buƙatar haɗa jihar Kano da gwamnatin tarayya domin hanzarta samar da ci gaba.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fada da ya koma APC

Gwamna Abba ya yi magana kan komawarsa APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron karbarsa zuwa jam'iyyar APC Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Abba Kabir ya yi jawabi ga dumbin mutane

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga dumbin jama'a a wurin taron karbarsa zuwa jam'iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Abba Kabir Yusuf ya ce jihar Kano tana da girma da kuma muhimmancin da ba za ta zauna a gefe tana tafiya ba tare da gwamnatin tarayya ta fuskar siyasa ba.

"Wannan mataki ne na sanya Kano a matsayin da za ta iya shiga cikin harkokin ci gaban kasa baki ɗaya, sannan mu samar wa ƴan jihar kyakkyawar makoma."

Kara karanta wannan

Shettima ya fadi muhimmancin Kano ga APC bayan karbar Gwamna Abba zuwa jam'iyyar

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Abba ya ce burin kansa ya koma APC ba

Gwamnan ya kara da cewa matakin ba don wani buri na kashin kansa ba ne, a’a, nauyi ne da ya rataya a wuyansa na yi wa al’ummar jihar hidima.

Ya jaddada cewa dole ne Kano ta shiga cikin tsarin nan na 'Renewed Hope Agenda' na Shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa gyare-gyaren da shugaban kasar yake yi suna bukatar jagoranci mai ma'ana da jajircewa wajen tabbatar da su domin kasa ta amfana.

“Tare da goyon bayan babbar jam’iyyar mu da kuma haɗin kan gwamnatin tarayya, jihar Kano ta fi samun damar ci gaba cikin amana da kwanciyar hankali."

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba ya yi godiya

Gwamna Abba ya kuma nuna godiyarsa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da gwamnonin jihohin Jigawa, Sokoto, Kaduna, Katsina, Borno, Yobe, da Plateau saboda halartar taron da kuma nuna goyon baya ga gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Manyan jam'iyyar APC da aka gani wajen tarbar gwamna Abba daga NNPP a Kano

Haka kuma, ya jinjina wa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kuma mambobin majalisar tarayya da na jiha bisa nuna haɗin kansu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi godiya ga Kashim Shettima
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Kashim Shettima wajen karbarsa zuwa jam'iyyar APC Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Ya ce halartar su wurin taron, tana nuna haɗin kai da kuma kuduri guda na ganin an samu daidaiton siyasa da ci gaba mai dorewa a Kano.

A yayin taron, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da su ba gwamnan goyon baya, inda ya yaba da yadda shugabanni da magoya baya suka fito da yawa a wurin taron.

Shettima ya karbi Gwamna Abba zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya karbi Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.

Kashim Shettima ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron karbar gwamnan wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha.

gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi, Kaduna, Sokoto da Imo, tare da sauran manyan shugabannin jam’iyya da ’yan majalisar tarayya, sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng