Gwamnan APC da ake Fatan Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa bayan 2027
- Gwamnonin APC sun fara nuna alamun goyon bayan gwamnan Imo, Hope Uzodimma ya dawo shugaban majalisar dattawa bayan zaben 2027
- An fara bayyana haka ne gabanin babban taron jam'iyyar APC na kasa da za a gudanar kafin zaben shekarar 2027 da za a yi
- Rahoto ya nuna cewa gwamna Hope Uzodimma ya yi magana game da fatan alheri da aka masa, inda ya ce hakan abin farin ciki ne matuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gabanin tarukan zaɓen shugabannin na jam’iyyar APC mai mulki, gwamnonin jam’iyyar sun fara wani yunƙuri a ɓoye domin karɓe cikakken iko da tsarin jam’iyyar a faɗin ƙasa.
An ce matakin na da nufin shimfiɗa tubali mai ƙarfi domin sarrafa jam’iyyar a shirin ɗaura shugaban kungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma, a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 11.

Source: Facebook
Rahoton Leadership ya nuna cewa manufar gwamnonin, a cewar majiyoyi, ita ce samun iko da majalisar dattawa ta 11 bayan rantsar da ita a watan Yuni 2027.
Gwamna Uzodimma zai nemi Sanata
An ce gwamna Uzodimma da aka zaɓa karo na biyu 2023 yana shirin sayen fom ɗin takarar Sanata tun yana kan kujerar gwamna, kasancewar doka ba ta hana shi shirin neman wata kujera ba yayin da yake kan mulki.
Majiyar ta ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan shirin, kuma zai mayar da hankali kan neman shugabancin majalisar dattawa, tare da goyon bayan takwarorinsa, idan ya lashe zaɓen Sanata.
Sai dai majiyar ta lura cewa nasarar shirin zai tabbata ne da amincewar shugaban ƙasa, da kuma barin gwamnonin su taka rawa wajen tantance shugabannin majalisar ƙasa ta gaba.
Martanin gwamna Hope Uzodimma
Amma da aka tuntubi Uzodimma ya ce bai san da wannan yunƙuri daga takwarorinsa ba, sai dai ya karɓi fatan zama shugaban majalisar dattawa na gaba da budaddiyar zuciya.
Ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai, Hon. Oguwike Nwachuku, gwamnan ya ce yunƙurin takwarorinsa na nuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu.
Ana ganin cewa idan Uzodimma ya koma majalisar dattawa, za a ɗauke shi a matsayin babban Sanata domin ya taɓa yin Sanata daga 2011 zuwa 2019 kafin ya tsaya takarar gwamna ya kuma yi nasara.

Source: Facebook
Tun daga 2007, majalisar dattawa ta zama mataki na gaba a siyasa ga gwamnonin da suka kammala wa’adin su na shekaru takwas.
Sai dai wata majiya mai kusanci da fadar shugaban ƙasa ta shaida cewa matakin wata hanya ce ta sharar fage a hankali domin nasarar shugaban kungiyarsu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu tabbaci kai tsaye ba ko shugaba Bola Tinubu ya amince da yunƙurin gwamnonin APC na taka rawa sosai wajen tantance ’yan takarar majalisar ƙasa daga jihohinsu.
Majalisa za ta yi zama ranar Talata
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar kasa za ta yi zama na musamman kan ranar zaben gwamnoni da shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan
Jigon APC ya tono abin da aka rufe, ya fadi abin da Tinubu ke tsoro game da zaben 2027
Hakan na zuwa ne bayan al'ummar Musulmi sun yi korafi game da sanya ranar zaben shugaban kasa na 2027 a watan Ramadan.
Wata majiya daga majalisar dattawa ta bayyana cewa ana kyautata zaton cewa za a iya mayar da ranar zaben zuwa ranar 13 ga Fabrairun 2027.
Asali: Legit.ng

