Sanatoci 2 da Yan Majalisar Wakilai 3 Sun Canza Jam'iyya, Sun Koma Jam'iyyar APC

Sanatoci 2 da Yan Majalisar Wakilai 3 Sun Canza Jam'iyya, Sun Koma Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar APC ta karbi 'yan majalisar tarayya biyar daga jihar Osun da suka sauya sheka daga PDP a wani gangamin taro da aka shirya
  • Ministan Harkokin Sufurin Teku, Gboyega Oyetola ne ya jagoranci karbar masu sauya shekar a taron da ya gudana a Osogbo ranar Asabar
  • Oyetola ya tabbatar wa yan Majalisar cewa su dauka sun dawo gida ne domin babu wani bako a jam'iyyar APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - ’Yan Majalisar tarayya biyar da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar PDP, a ranar Asabar, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a Jihar Osun.

An tarbe su ne a birnin Osogbo ta hannun shugabannin jam’iyya, mambobi da magoya baya karkashin jagorancin Ministan Harkokin Sufurin Teku, Alhaji Gboyega Oyetola.

Taron APC.
Gangamin da APC ta shirya domin tarbar sanatoci da yan majalisa a Osun Hoto: Osun APC Youth
Source: Facebook

Yan Majalisa 5 sun sauya sheka zuwa APC

Kara karanta wannan

An kada hantar Kwankwaso, Barau ya yi alkawari ga Abba, Tinubu kan zaben 2027

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da: Sanata Francis Fadahunsi (Osun ta Gabas) da Sanata Olubiyi Fadeyi (Osun ta Tsakiya).

Sai kuma mambobin Majalisar wakilan tarayya uku, wadanda suka kunshi Hon. Omirin Olusanya (Mazabar Ijesa ta Arewa), Hon. Wole Oke (Mazabar Ijesa ta Arewa) da Hon. Taofeek Ajilesoro (Mazabar Ife ta Tsakiya).

A gangamin da aka shirya yau Asabar a Osogbo, Oyetola, ya ce a APC babu baƙo, yana mai cewa zuwan sababbin mambobin zai ƙarfafa shirin jam’iyyar na sake karɓar ragamar mulkin Osun da dawo da martabar shugabanci.

Oyetola ya jaddada kudirin APC

“Mun taru ba wai don tarbar sababbin mambobi kadai ba, har da jaddada yakininmu cewa hanya mafi dacewa zuwa ci gaba, kwanciyar hankali da shugabanci mai nagarta tana cikin APC.
"A APC babu baƙi, mu dangi guda ne, zuwan ku ya ƙara mana ƙwarin gwiwa a kokarin mu na sake karɓar Osun da dawo da martabar shugabanci,” in ji shi.

Oyetola ya kuma ce nasarorin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu tun bayan hawansa mulki sun kafa tubali mai ƙarfi don farfaɗowar Najeriya, in ji rahoton Gazette NGR.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai

“Saboda haka ne muke alfaharin cewa za mu sake goyon bayan Shugaba Tinubu ya zarce wa’adi na biyu a 2027 domin ƙarfafa waɗannan nasarori da tabbatar da ɗorewar ci gaba,” in ji shi.
Shugaban APC.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe a hedkwatar jam'iyya da ke Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Shirye-shiryen zaɓen gwamna 2026

Oyetola ya buƙaci mambobin jam’iyyar su haɗa kai domin samun nasara a zaɓen gwamnan da za a gudanar a ranar 8 ga Agusta, 2026 a jihar Osun.

“Zaɓen gwamnan 2026 na gab da zuwa. Manufarmu a fili take, kwace jihar Osun da dawo da shugabanci irin wanda jama'a ke bukata," in ji shi.

APC ta yi zargin ana karya allunan tallar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi gargadi game da zargin ruguza allunan tallan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a sassan Zamfara.

A cikin wata sanarwa da kakakin APC a Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, jam’iyyar ta ce ana zargin cewa irin waɗannan ayyuka sun daɗe suna faruwa.

APC ta zargi gwamnatin jihar Zamfara da hannu a lalata allunan tallar shugaban kasa, tana mai cewa ba za ta duba ido tana kallo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262