Sanata Ndume Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Ja Kunnen APC kan Jam'iyyar ADC
- Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya aika da sakon gargadi ga jam'iyyarsa ta APC
- Ali Ndume ya sanar da jam'iyyar APC abin da ya kamata ta yi wa sabuwar hadakar 'yan adawa ta ADC wadda ke son samun madafun iko
- Sanata Ndume ya bayyana cewa sauya shekar da 'yan siyasa suke yi daga wannan jami'iyya zuwa wancan ba shi ba ne tabbacin samun goyon baya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya gargaɗi jam’iyya mai mulki ta APC da kada ta yi wasa da ’yan Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.
Sanata Ali Ndume ya kuma ja kunnen APC kan kada ta raina sabuwar haɗakar ’yan adawa da ke ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Source: Twitter
Ali Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairun 2026.
Wace shawara Ndume ya ba APC?
Sanata Ndume ya ce yayin da ’yan siyasa ke sauya sheka tsakanin jam’iyyu, talakawan Najeriya suna kallon duk abin da ke faruwa, kuma su ne za su yanke hukunci a rumfunan zaɓe.
“Kada a yi wasa da jam’iyyar adawa ta ADC. Kada a raina kowane dan adawa. Kun ga abin da Obi ya yi a lokacin da ya gabata; babu wanda ya yi tunanin zai iya samun wannan yawan ƙuri’un. Saboda haka, kada mu raina kowa."
- Sanata Ali Ndume
Ndume ya yi tsokaci kan sauya sheka
Ya bayyana cewa sauya shekar da ’yan siyasa ke yi daga wannan jam’iyya zuwa waccan bai kamata a ɗauke shi a matsayin samun goyon bayan jama’a ba, yana mai jaddada cewa masu zaɓe sun kara zama masu sa ido a yanzu.
“’Yan siyasa ne ke sauya sheka, amma har yanzu jama’a ba su sauya sheka ba. Suna nan suna kallo. Kuma idan kuka yi wasa da ’yan Najeriya, za ku fuskanci sakamako mai tsauri."
- Sanata Ali Ndume
Sanata ya ce 'yan Najeriya ba sa jin dadi
Ndume ya lura cewa ’yan Najeriya da dama ba sa jin daɗin yadda ake gudanar da mulki a halin yanzu, amma wasu lokuta mutane sun fi son abin da suka sani fiye da abin da ba su sani ba.
“’Yan Najeriya ba sa gamsuwa da abin da ke faruwa. Amma wani lokacin mutane sun fi son abin da suka saba da shi fiye da abin da ba su sani ba."
- Sanata Ali Ndume
Sanatan ya ce har yanzu gwamnatin APC tana da lokacin gyara kura-kuranta, amma ya yi gargaɗin cewa lokaci yana kurewa.
“Na yi amanna shugaban ƙasa zai iya gyara abubuwa, amma lokaci yana ƙurewa."
- Sanata Ali Ndume

Source: Facebook
Ya bayyana cewa yayin da ’yan hamayya suka mayar da hankali kan babban zaɓe mai zuwa, babban abin da ya dame shi shi ne shugabanci na gari da kuma cika alkawuran da ya ɗauka.
“Na fi damuwa da shugabanci na gari. Ban damu sosai da batun cin zaɓe mai zuwa ba. Na damu ne da yadda zan sauke nauyin da mutane na suka ɗora mini."
- Sanata Ali Ndume
Amaechi ya ba ADC shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ba jam'iyyar adawa ta ADC shawara.
Amaechi ya bukaci jam'iyyar ADC da ta tsaya ta duba da kyau ta dauko mutumim da ya fi dacewa wanda zai iya gamsar da 'yan Najeriya cewa abubuwa za sauya.
Tsohon Ministan ya yi gargadin cewa zai iya zama abu mai wahala ga jam’iyyar ADC ta tallata dan takarar shugaban kasa daga Arewa ga masu zabe a Kudancin Najeriya.
Asali: Legit.ng


