El Rufai Zai Tsaya Takarar Shugaban Najeriya a 2027? Tsohon Gwamna Ya Bada Amsa

El Rufai Zai Tsaya Takarar Shugaban Najeriya a 2027? Tsohon Gwamna Ya Bada Amsa

  • Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na yin takarar shugaban kasa a 2027, amma bai kore yiwuwar takarar gaba daya ba
  • Tsohon gwamnan ya koka kan yadda ake karkatar da dukiyar jama'a yayin da yan Najeriya ke shan wahala a karkashin wannan gwamnati
  • Saboda haka, El-Rufai ya ce kofar sa a bude take idan har shugabannin jam'iyyarsa suka bukaci ya tsaya takara a zaben shekarar mai zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fito fili ya bayyana matsayinsa game da yin takarar shugabancin ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Malam Nasir El-Rufai ya ce akwai wadanda suka cancanci yin takara fiye da shi, amma kuma zai iya neman kujerar shugaban kasar bisa wasu dalilai.

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Abin da El Rufai ya fadawa Atiku game da Tinubu a Abuja

Malam Nasir El-Rufai ya yi magana kan yin takarar shugaban kasa a 2027
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a dakin watsa shirye-shiryen Arise News. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Matsayar El-Rufai kan takarar shugaban kasa

A wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Arise News a yau Juma'a, El-Rufai ya magantu kan makomar siyasarsa.

Ya bayyana cewa duk da matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta, har yanzu bai yanke shawarar tsayawa takara a hukumance ba.

"Ina tabbatar maka cewa a halin yanzu ni ba ɗan takarar kowane ofis ba ne a faɗin ƙasar nan.
"Ya kamata a ce zuwa yanzu na yi ritaya daga harkar siyasa baki ɗaya bayan na kammala wa'adin mulki na. Amma ganin yadda 'yan Najeriya ke shan wahala a sassan ƙasar nan, yana karya mini zuciya matuƙar gaske.
"Muna ganin yadda ake karkatar da dukiyar jama'a zuwa hannun wasu tsirarun mutane yayin da talakawa ke cikin matsananciyar yunwa.
"Sai dai duk da haka, har yanzu ban yanke shawarar neman kujerar shugaban kasa ba. Babu wannan a cikin tsari na har yanzu.

"Akwai wadanda suka cancanta" - El-Rufai

Kara karanta wannan

Bayan ziyartar El Rufai, Atiku ya tona shirin da APC ke yi kan jam'iyyar ADC

Ko da aka tambayi tsohon gwamnan na Kaduna game da ko akwai sha'awar yin takarar a zuciyarsa, sai cewa ya yi:

"Ko kadan, babu. Akwai mutanen da suke da kwarewa da suka nuna sha'awar yin takarar. Ina da yakinin cewa za su yi abin da ya dace.

An kuma tambayi El-Rufai ko maganarsa na nufin 'ba zai taba neman takara ba a rayuwarsa,' inda tsohon gwamnan ya ba da amsa da cewa:

"A harkar siyasa ba a cewa 'ba zan taɓa yi ba', domin sa'o'i 24 lokaci ne mai tsawo sosai. Ko da na ce ba zan taba nema ba a yau, abubuwa na iya sauya wa gobe.
"Misali, idan shugabannin jam'iyyata suka zo gare ni, suka ce, 'Nasir, dukkan 'yan takara sun janye, kuma kai muke so ka yi takara,' to ka ga a nan lamarin ya sauya."
Malam Nasir El-Rufai ya ce ya damu matuka da halin da 'yan Najeriya suke ciki.
Mallam Nasir El-Rufai, zaune a kan kujerar Gwamnan Kaduna a ranar 15 ga Yuni, 2019. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Matsayin El-Rufai kan halin da kasa ke ciki

El-Rufai ya bayyana damuwarsa kan yadda ake tafiyar da arzikin Najeriya, yana mai cewa abin yana ci masa tuwo a ƙarya.

Ya lura cewa 'yan Najeriya suna fuskantar ƙalubale ba tare da la'akari da addini, ƙabila, ko kuma yankin da mutum ya fito ba.

Kara karanta wannan

Yadda alakar El-Rufai da Ribadu ta lalace shekaru bayan yi masa takwara

Kalli bidiyon hirar wadda Imran Muhammad ya wallafa a shafinsa na X a nan kasa:

El-Rufai zai mika kansa ga EFCC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mallam Nasir El-Rufai ya musanta rade-radin cewa ya gudu kasar waje ne domin ya tsere wa binciken cin hanci da rashawa da ake masa.

Yayin da yake a ƙasar, hukumar EFCC ta aika da takardar gayyata zuwa gidansa a watan Disamba na shekarar 2025, wanda hakan ya jawo raɗe-raɗin cewa za a iya kama shi.

A tattaunawa da manema labarai, El-Rufai ya bayyana cewa zai je ofishin EFFC a ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, inda har ya ce zai amsa dukkan tambayoyi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com