Nasir El Rufa'i: "Ina Kada Hantar Masu Mulkin Najeriya"

Nasir El Rufa'i: "Ina Kada Hantar Masu Mulkin Najeriya"

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce masu mulki ba sa jin daɗin dawowarsa Najeriya da ga Cairo saboda wasu dalilai
  • Ya bayyana cewa gwagwarmayar siyasa domin sauke gwamnati ta fara ne yanzu, kuma ba zai saurara ba har sai an kayar da shugaban kasa
  • Tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa babu wani sabani a tsakaninsa da Shugaban kasa kai tsaye domin bai taba aiki da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa masu mulki a yanzu ba sa jin daɗin dawowarsa gida Najeriya.

Ya bayyana cewa duk ya firgita su, tare da jaddada cewa yanzu aka fara gwagwarmayar siyasa domin sauke gwamnatin da ke kan mulki.

Tsohon gwamnan Kaduna ya ce yana tsorata masu mulki
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i Hoto: Bayo Onanuga/Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Nasir El-Rufa'i ya bayyana haka ne bayan da aka yi yunƙurin kama shi a filin jirgin Abuja.

Nasir El-Rufa'i ya yi wa gwamnati barazana

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Nasir El-Rufa'i ya ce tun bayan kama dare wa karagar mulki, ya shiga cikin jerin mutane kalilan a Najeriya da ke adawa da gwamnati.

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Abin da El Rufai ya fadawa Atiku game da Tinubu a Abuja

Ya ce:

“Kun san da wannan gwamnati ta zo, ni na kasance cikin ’yan kaɗan da suka fito suka ce za mu yi adawa da ita kuma mu kore ta daga mulki."

Ya ƙara da cewa da a ce akwai wata hujja ta gaskiya a kansa kamar yadda ake yi wa wasu ikirari, da tuni an warware batun zarge-zarge da ake yi masa.

Tsohon gwamnan Kaduna na so a lallasa APC a zaben 2027
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

Ya ce:

“Da suna da wani abu a kaina kamar yadda suke cewa suna da shi a kan wasu, da tuni an gama da maganar. Amma ko za ku zarge ni, ku tabbata kun tabbatar da zargin. Ina jira; duk wanda ya gayyace ni zan je."

Dalilin El-Rufai na adawa da gwamnatin Tinubu

Tsohon gwamnan, wanda da shi aka kafa gwamnati ya bayyana cewa sabanin ra'ayi da bambancin manufofi ne ya sanya shi fara sakun saka da Tinubu.

Ya ce:

“Manufofinmu ne suka bambanta, domin lokacin da na tsaya tare da wannan gwamnati ko jam’iyya, abin da muke gani a yanzu ba shi muka gani a wancan lokacin ba. Sun sauya. Idan manufofinka sun bambanta da nawa, mu rabu lafiya. Kowa ya tafi ya ta kansa. Babu faɗa."

Kara karanta wannan

'Ku taimaka mani': Ɗan Arewa ya roki Najeriya bayan tilasta masa shiga soja a Rasha

Game da alaƙarsa da Bola Tinubu, El-Rufai ya ce babu wata matsala ta kashin kai a tsakanina da Shugaban kasa.

Ya ce:

“Ba ni da wata matsala da Tinubu domin ba mu taɓa yin hulɗa tare ba. Tinubu ba mutumina ba ne; ba mu taɓa yin siyasa tare ba. Mun haɗu ne a APC lokacin da Buhari ya fito ya ci zaɓe. Kuma Tinubu ya bayar da gudummawa."

Alakar Uba Sani da Nasir El-Rufai

Bayan batun dangantakarsa da Bola Ahmed Tinubu wanda El-Rufai ya tallata da kyau a lokacin yana gwamnan Kaduna, ya yi maganar Uba Sani.

Dangane da magajinsa a Kaduna, Uba Sani, ya ce:

“Game da Uba Sani, yaro na ne a siyasa. Shi da kansa ya sha faɗin cewa mutumina ne. Ba mu da saɓani; manufofinmu ne kawai suka bambanta.”

Dole mu kawar da azzalumar gwamnati - El-Rufa'i

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da jami'an tsaro suka yi yunkurin kama shi ya karbi bakuncin Atiku Abubakar a gidansa, inda suka tattauna.

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu saboda yunkurin kama El Rufa'i

El-Rufai ya shaidawa Atiku cewa abin da ya faru da shi a filin jirgi ya kara tabbatar da cewa dole 'yan adawa su kafa gwamnati a 2027, a kawar da gwamnatin Tinubu a filin zabe.

Tsohon gwamnan ya kuma fadawa Atiku cewa bai kamata su runtsa ba har sai sun kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulkin Najeriya tare da kafa sabuwar gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng