Yunkurin Kama El Rufa'i: Reno Omokri Ya Jero 'Zunuban' Tsohon Gwamna a Kaduna

Yunkurin Kama El Rufa'i: Reno Omokri Ya Jero 'Zunuban' Tsohon Gwamna a Kaduna

  • Ambasada mai jiran gado, Reno Omokri, ya goyi bayan jami'an gwamnatin Najeriya da ke kokarin tuhumar tsohon gwamnan Kaduna
  • A ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairu na shekarar 2026 ne jami'an tsaro suka tare Nasir El-Rufa'i a filin jirgin Abuja bayan dawowarsa daga Cairo
  • A kalamansa bayan gari ya dauki zafi a kan batun, Reno Omokir ya zargi El-Rufa'i da zalunci da take hakkokin 'yan adam a lokacin yana gwamna

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Ambasada mai jiran gado, Reno Omokri, ya sake bankado batutuwa masu sosai rai game da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Martaninsa na zuwa ne a lokacin da kasar nan ta dauki zafi a kan batun yunkurin kama El-Rufa'i a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairu na shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu a bayan yunkurin kama El Rufa'i

Omokir ya zargi El-Rufa'i da zalunci a mulkinsa
Reno Omokir, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i Hoto: Reno Omokri/Nasir El-Rufai
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairu,2026 Omokri ya waiwayi shekaru takwas da El-Rufai ya yi yana mulki.

Omokir ya caccaki mulkin El-Rufa'i

Reno Omokir, tsohon hadimin Shugaban kasa ya zayyana zarge-zargen take hakkin bil’adama, murkushe masu adawa da kuma rusa gidaje da ake zargin El-Rufa'i ya jagoranta.

Omokri ya wallafa hoto mai tayar da hankali na Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, yana mai cewa an jefa jagoran shi'a a cikin mummunan hali a lokacin mulkin El-Rufai.

Ya kara da cewa mutane 347 mabiya Shi’a, daga ciki har da mata da kananan yara har ma da jarirai, sun rasa rayukansu a wannan lokaci, duk da cewa wasu alkaluma marasa tushe sun kai adadin zuwa kusan 1,000.

Omokri ya ce:

“Bayan mayar da Sheikh Zakzaky cikin irin wannan mummunan hali na rashin tausayi, an kashe maza, mata, yara da jarirai mabiya Shi’a 347 a ƙarƙashin Nasir el-Rufai."

Kara karanta wannan

Sanata Ahmad Babba Kaita: Yadda masoya suka hana jami'ai tafiya da El Rufa'i

Omokri ya zargi El-Rufa'i da zalunci

Ya kuma ambaci batun Abubakar Idris, da aka fi sani da Dadiyata da ya shawara wajen sukar gwamnati, wanda aka sace kuma har yanzu shiru.

Omokri, wanda ya taba zama hadimi a karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya zargi El-Rufai da rusa kadarorin wasu ‘yan siyasa kamar Sanata Suleiman Hunkuyi da Alhaji Inuwa Abdulkadir.

Reno Omokri ya zargi El-Rufa'i da rushe gidajen yan adawa
Reno Omokir, tsohon hadimin Shugaban kasa Goodluck Jonathan Hoto: Reno Omokri
Source: Facebook

Ya ce:

“Nasir el-Rufai ya kama ‘yan jarida da masu fafutuka da dama saboda sun ruwaito labarai marasa dadi a kansa, daga cikinsu har da Jacob Onjewu Dickson, Segun Onibiyo, Midat Joseph da Audu Maikori."

Omokri ya soki ikirarin El-Rufai na cewa ana takura masa, yana mai cewa ana tuhumarsa ne bisa zarge-zargen aikata laifuffuka, da suka hada da zargin batan N423bn.

Ya ce:

“Nasir el-Rufai yana da hannu a zargin sace Naira biliyan 423 a lokacin mulkinsa kamar yadda Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta bayyana. Ba ya sama da doka ko kamu."

Kara karanta wannan

Yunkurin kama El Rufai, lauyoyi sun zayyana dokoki 5 da jami'an tsaro suka take

Ya ce bai kamata a manta da tarihin zargin murkushe masu adawa da aikata ta’asa ba, yana mai jaddada cewa dole ne a hukunta kowa bisa doka.

Alakar El-Rufa'i ta Nuhu Ribadu ta lalace

A baya, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi APC da zalunci bayan ficewarsa zuwa jam'iyyar ADC, yana mai cewa ana yi masa bita da kulli.

El-Rufa'i ya nuna mamaki a kan sauyin halayen Malam Nuhu Ribadu duk da kyakkyawar alakar da suka taba yi a baya wanda ya sauya kuma ya yi tsami a yanzu.

Ya ce ruwa ba zai ci El-Rufai ba, yana mai jaddada cewa Allah na tare da shi, tare da kalubalantar Ribadu ya bayyana dalilin da ake zarginsa da aikata laifuffuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng