Biki Wan Shagali: Tinubu da Kansa Zai Tarbi Gwamna Abba zuwa APC, an Sa Lokaci
- Bayan rajista da jam'iyyar APC, an shirya babban taro domin karbar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a hukumance
- Jam'iyyar APC ta shirya babban taro tare da gayyato manyan baki domin halartar bikin tarbar Gwamna Abba zuwa cikinta
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, na daga cikin manyan bakin da za su halarci gagarumin bikin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tarbi Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC a hukumance.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai isa Kano ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026 domin karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance zuwa jam’iyyar APC.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kasar zai tarbi gwamnan ne a wani gagarumin biki da aka tsara gudanarwa a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.
Tinubu da jiga-jigai za su tarbi Abba zuwa APC
An tsara cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da gwamnonin APC da dama za su halarci taron.
Shugabannin jam’iyyar sun bayyana taron a matsayin wani babban taron siyasa da nufin karfafa ikon APC a shiyyar Arewa maso Yamma.
Shugaban APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce taron zai zama alama ta karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance zuwa jam’iyya mai mulki, jaridar Tribune ta kawo labarin.
Ya siffanta wannan cigaba a matsayin wani babban mataki ga APC a Kano, wacce aka dade ana kallo a matsayin daya daga cikin muhimman sansanonin siyasa a Najeriya.
An kafa kwamitoci don bikin tarbar Abba
Abdullahi Abbas ya ce an yi shirye-shirye na musamman domin tabbatar da an gudanar da taron lami lafiya, inda aka kaddamar da kwamitoci da dama domin daidaita harkokin tsaro sufuri, da kuma gangami.
Kwamitin tsaro mai mambobi 15, karkashin jagorancin Kanal Umar Malami, tare da Darakta janar na ayyuka na musamman a matsayin sakatare, zai kula da shirye-shiryen tsaro.
Kwamitin samar da wuri mai mambobi 16, karkashin jagorancin Hon. Bala Mohd Gwagwarwa, tare da Engr. Umar Abdullahi Ganduje a matsayin sakatare, zai kula da kayayyakin aiki a filin wasan.

Source: Facebook
Harkokin yada labarai da tuntubar jama'a za su kasance a karkashin kwamitin yada labarai mai mambobi 15 karkashin jagorancin Hon. Muhammad Garba.
Hakazalika, kwamitin lafiya da tsafta, karkashin jagorancin Dr. Abubakar Labaran, zai kula da ayyukan lafiya da na matakin gaggawa.
Kwamitin ladabi da tsare-tsare, karkashin jagorancin Hon. Abdullahi Rogo, zai kula da harkokin karbar manyan baki.
Domin tabbatar da fitowar jama'a da yawa, an kuma kafa kwamitin gangami mai mambobi 20 karkashin jagorancin Hon. Mohd Bello Butu-Butu.
'Dan majalisar PDP ya sauya sheka zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe ta rage karfi, bayan dan majalisar wakilanta ya fice daga cikinta.
Hon Abdullahi El-Rasheed wanda ke wakiltar Dukku/Nafada a majalisar wakilai ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan ficewa daga PDP.
'Dan majalisar ya danganta matakinsa na shiga APC da salon jagoranci na gari na Gwamna Inuwa Yahaya, da manufofinsa masu alaka da jin dadin jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

