Atiku Ya Ziyarci El Rufai da Dare bayan Ya Sha da Kyar a Filin Jirgin Sama

Atiku Ya Ziyarci El Rufai da Dare bayan Ya Sha da Kyar a Filin Jirgin Sama

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyara ta musamman ga Nasir El-Rufai bayan hargitsin a filin jirgin sama
  • Atiku ya nuna masa cikakken goyon baya, yana zargin gwamnatin Bola Tinubu da kokarin kawo mulkin kama-karya
  • Ziyarar na zuwa ne bayan kokarin jami’an tsaro na cafke El-Rufai, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce da rikici

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Jim kadan bayan hargitsin da ya faru a filin jirgin sama, Atiku Abubakar ya kai ziyara ta musamman ga Nasir El-Rufai a gidansa.

Atiku ya kai ziyara ga El-Rufai ne domin nuna masa goyon baya dari bisa dari bayan abin da ya faru da shi a filin jirgin sama.

Atiku ya ziyarci El-Rufai bayan kokarin cafke shi
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da Atiku Abubakar. Hoto: Nasir El-Rufai, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani bidiyo da Abdulaziz Na'ibi Abubakar, daya daga cikin masoyan Atiku ya wallafa a shafin X a daren jiya Alamis 12 ga watan Faburairun 2026.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya ce rikicin duniya da mai rai ake, zai buga da Tinubu da APC

An yi yunkurin cafke El-Rufai

Wannan ziyara na zuwa ne bayan kokarin da jam'ian tsaro suka yi na cafke tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a Abuja.

Lamarin ya hargitse yayin da El-Rufai da magoya bayansa suka ki amincewa da shirin cafke shi jim kadan bayan shigowa Najeriya daga ketare.

Hakan bai rasa nasaba da yawan sukar gwamnatin Bola Tinubu da tsohon gwamnan ke yi wanda a yan kwanakin nan abin sai karuwa yake yi.

Daga cikin hirarrakin da yake yi, ya ambaci cewa ana shirin kama shi idan ya dawo Najeriya wanda kuma hakan ya tabbata.

Atiku ya ziyarci El-Rufai a gidansa

Yayin ziyarar, Atiku Abubakar ya bayyana goyon bayansa ga El-Rufai dari bisa dari game da halin da ake ciki da kuma lalacewar kasa.

Ya ce:

"Wannan gwamnati ba ta da niyyar ta bar dimukradiyya ta dore, tana son kawo mana mulkin kama-karya da na cin mutunci yadda ba wani dan Adam da yake da wani 'yanci.

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru a filin jirgi, El Rufai zai gurfana a gaban hukumar EFCC

"Mu 'yantattu ne, haka Allah ya halicce um, ba mu ga dalilin da za ta dauke mana hakkin da Allah ya ba mu ba.
"Malam ina mai tabbatar maka kana da cikakken goyon bayanmu, dukanmu mun amince a bin tafarkin dimukradiyya da dokokin kasa."
Atiku ya ba El-Rufai tabbacin goyon bayansa
Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Tabbacin da Atiku ya ba El-Rufai

Atiku ya ba El-Rufai tabbacin cewa za su ci gaba da ba shi goyon baya da kuma tsare mutuncinsa da na magoya bayansu.

"Mu na shirye mu ba ka kowane irin taimako, mu tsare mutuncinka da mutuncin magoya bayanmu, muna yi maka barka da dawowa.
"Za mu ci gaba da wannan yaki na tabbatar da yanci da dorewar dimukradiyya, wannan APC mu muka kafa ta, amma sun kauce hanya shi yasa muka fita."

- Atiku Abubakar

El-Rufai zai ziyarci ofishin EFCC a Abuja

Mun ba ku labarin cewa Lauyan Malam Nasiru El-Rufai ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan zai amsa gayyatar EFCC a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu, 2026.

Barista Ubong Esop Akpan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan yunkurin da jami'an tsaro suka yi na kama El-Rufai a filin jirgin sama a Abuja.

Ya ce abin da jami'an tsaron suka yi ya saba wa kundin tsarin mulki, yana mai cewa sun sanar da EFCC halin da ake ciki tun farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.