Karamar Magana Ta Zama Babba, Kwankwasiyya Ta Aika Sako ga Majalisar Amurka
- Kwankwasiyya ta aika sako Amurka bayan sanya sunan Kwankwaso a jerin wadanda kasar ke zargi da hannu a tauye hakkin addini a Najeriya
- Tafiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa ba a jihar Kano kadai aka kaddamar da shari'a ba, don haka ware mutum daya ba adalci ba ne
- Ta bukaci majalisar dokokin Amurka ta gaggauta cire sunan Kwankwaso daga cikin kudirinta domin hakan na iya yi masa illa a siyasance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kwankwasiyya ta yi kira ga Amurka ta cire sunan jagoranta, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso daga cikin jerin wadanda ake zargi da tauye hakkin addini.
Kwankwasiyya ta yi watsi da wani yunkuri da ‘yan majalisar Amurka biyar suka fara domin saka sunan Kwankwaso, cikin jerin wadanda za a sa wa takunkumi saboda tauye yancin addini.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce 'amarin ya biyo bayan gabatar da kudirin dokar Nigeria Religious Freedom and Accountability Act 2026 (HR 7457) a Majalisar Dokokin Amurka a ranar Talata.
Idan kudirin ya zama doka, zai tilasta wa Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da Ma’aikatar Kuɗi ta ƙasar su kakaba takunkumin hana biza kan Kwankwaso da wasu ƙungiyoyin fulani kamar MACBAN, bisa zargin hannu a muzguna wa Kiristoci.
Kwankwasiyya ta maida martani
A martanin da ta yi ranar Alhamis, Kwankwasiyya ta bayyana saka sunan tsohon gwamnan Kano a cikin kudirin a matsayin kage marar tushe, wanda aka sa siyasa a ciki, tare da buƙatar a cire sunansa nan take.
Mai magana da yawun 'yan Kwankwasiyya, Habibu Sale Mohammed, ya ce:
“Muna tabbatar wa jama'a cewa waɗannan zarge-zarge ba su dace da tarihin rayuwa da hidimar da Sanata Kwankwaso ya yi ba.”
Ƙungiyar ta mayar da martani ga zargin da ɗan majalisar Amurka Riley Moore ya yi, wanda ake cewa ya danganta Kwankwaso da tsattsauran ra’ayi saboda aiwatar da tsarin Shari’a a lokacin mulkinsa.
Kwankwaso kadai ya yi tsarin shari'a?
Kwankwasiyya ta ce tsarin Shari’a da aka kafa a wasu jihohin Arewa na cikin tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ba Kano kaɗai ba ce ta aiwatar da shi, balle a ce mutum ɗaya ne ya yi.
Ta ƙara da cewa ware Kwankwaso shi kaɗai alhali irin wannan tsari yana aiki a wasu jihohi ya jawo tambayoyi kan sahihancin hujjojin da aka dogara da su, in ji rahoton Daily Trust.
Har ila yau, ta ambaci takarar shugaban ƙasa da ya yi a 2023 tare da Bishop Isaac Idahosa a matsayin hujjar yadda yake goyon bayan haɗin kan addinai da daidaiton ƙasa.

Source: Facebook
Sakon yan Kwankwasiyya ga Amurka
Kwankwasiyya ta buƙaci Majalisar Dokokin Amurka ta cire sunan Kwankwaso cikin kudirin, tana mai zargin cewa wasu na iya amfani da lamarin wajen biyan buƙatun siyasa ko ramuwar gayya.
Ta bayyana Kwankwaso a matsayin “mai kishin ƙasa, ɗan dimokuraɗiyya kuma jigo mai kishin haɗin kai,” tare da nuna kwarin gwiwa cewa idan aka yi bincike, gaskiya za ta yi halinta.

Kara karanta wannan
Da mamaki: Bulama ya ga kuskuren amurka kan zargin kwankwaso da matsawa kiristoci
Fasto Idahosa ya aika sako ga Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa fasto kuma dan siyasa, Isaac Idahosa ya rubuta takarda ta musamman ga majalisar kasar Amurka game da Sanata Rabiu Kwankwaso.
Fasto Isaac Idahosa ya bayyanawa majalisar Amurka cewa a matsayinsa na wanda yake jagorantar harkokin addinin Kirista, ya san Kwankwaso mutumin kirki ne.
Idahosa ya ce ya tabbatar da jajircewar Sanata Kwankwaso wajen yi wa jama'a hidima da shugabanci ba tare da nuna bambanci ba.
Asali: Legit.ng

