Buba Galadima: Ana Son Hana Kwankwanso zuwa Kano saboda Zaben 2027
- Makusancin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya zargi APC Kano da kokarin hana Sanata Kwankwaso zuwa jiharsa
- Ya ce zancen da ake a yanzu, akwai takarda a Fadar Shugaban Kasa da ke neman a sanya wa Kwankwaso takunkumi don hana shi zuwa Kano
- A kan batun yunkurin wasu 'yan majalisar Amurka a kan Kwankwaso, Buba Galadima ya danganta zargin da batun zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagora a jam’iyyar NNPP kuma makusancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima, ya yi zargin cewa APC reshen Kano na yi wa Kwankwaso kulle-kulle.
Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin da wasu ‘yan majalisar Amurka suka danganta da Kwankwaso na cewa ya muzguna wa kiristoci.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da DCL Hausa, Buba Galadima ya ce a halin yanzu akwai wata takarda a gaban Fadar Shugaban Kasa da ake zargin na kokarin hana Kwankwaso zuwa Kano.
Ana zargin kokarin hana Kwankwaso zuwa Kano
Buba Galadima ya ce ana kokarin hana Kwankwaso zuwa garinsa ne saboda dalilai na siyasa, yana mai cewa hakan bai dace da tsarin doka da dimokuradiyya ba.
Ya kara da cewa suna jiran amsar da Fadar Shugaban Kasa za ta bayar kan takardar, da a cewarsa ke neman maimaita irin takurawar da aka taba yi wa Kwankwaso a baya.
Dangane da batun sanya sunan Kwankwaso cikin rahoton da ke neman hukunta wasu ‘yan Najeriya, Buba Galadima ya ce ba su yi mamaki ba.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Mu dai wannan zance bai zo mana da mamaki ba. Kodayake mu ba wannan muka zaci za a yi ba saboda akwai jita-jita da yawa.”

Kara karanta wannan
Da mamaki: Bulama ya ga kuskuren amurka kan zargin kwankwaso da matsawa kiristoci
Ya kara da cewa:
“Tun lokacin da aka matsawa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso cewa sai dole ya zo ya shiga jam'iyyar APC, kuma mutane da yawa, abokansa da masoya sun kai gwauro sun kai mari cewa idan bai shiga APC ba, akwai abubuwa da yawa na rashin dadi da ake tanadar masa.”
Ya ce wasu daga cikin makusantan Kwankwaso sun taba ba shi shawarar ya sauya sheka zuwa APC domin kauce wa matsaloli, yana mai cewa an yi masa barazana sosai.
Sai dai Buba Galadima ya jaddada cewa Kwankwaso ba shi da tsoro, kuma ya dage cewa ba zai sauya sheka ba sai an biya bukatun al’umma da ya gabatar.
Buba Galadima ya magantu a kan Abba
A baya, kun ji cewa jagora a NNPP, Buba Galadima, ya yi kakkausar suka kan sauya sheƙar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
A cewarsa, ficewar gwamnan daga NNPP a ranar 23 ga watan Janairun 2026, tare da komawarsa APC ya girgiza jam’iyyar da magoya bayanta a jihar baki daya.
Da yake mayar da martani kan sauya sheƙar gwamnan, Buba Galadima ya ce bai taba tsammanin Abba Kabir Yusuf zai bar NNPP ba, duba da taimakon da Kwankwaso ya yi masa.
Asali: Legit.ng
