Bayan Samun Mukami, Tsohon Mai Sukar Tinubu Ya Fadi Abin da Zai Sa Ya Zarce a 2027
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya nuna goyom bayansa ga tazarcen Mai girma Bola Tinubu a zaben 2027
- Reno Omokri wanda ya samu mukamin jakada ya bayyana cewa jam'iyyun adawa ba za su iya doke Shugaba Bola Tinubu ba
- Hakazalika, ya bayyana amfanin da 'yan Najeriya suka samu sakamakon sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya kawo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya yi magana kan tazarcen Mai girma Bola Tinubu a zaben 2027.
Reno Omokri ya bayyana cewa manufofin sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu sun cika muhimman alkawuran da ya dauka lokacin kamfe.

Source: Twitter
Reno Omokri ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Abin da Shugaba Tinubu ya ce kan Shettima yayin da ake jita jitar sauya shi a 2027
Reno Omokri ya yabi Shugaba Tinubu
Tsohon hadimin ya bayyana cewa alkawuran da Tinubu ya cika sun sanya ya zama abu mai wuya ga jam’iyyun adawa su iya kifar da shi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Ya bayyana yadda jam’iyyar APC ke dada karfafa ikonta a siyasance da kuma yadda alamun tattalin arzikin Najeriya ke inganta a matsayin shaida na nasarar shugaban kasar.
Omokri ya bayyana cewa damar da ’yan adawa suke da ita ta kara raguwa a yanzu tunda jam’iyyar APC tana iko da gwamnoni kusan 30, idan aka kwatanta da shekarar 2023 lokacin da take da gwamnoni kusan 20 kawai.
“Idan har ’yan adawa ba su iya kayar da Tinubu da gwamnoni kusan 20 ba a 2023, ta yaya za su iya kayar da shi a yanzu da yake da gwamnoni 30?"
“Idan har ’yan adawa ba su iya kayar da shugaban kasar ba a lokacin da bai cika alkawuran kamfen dinsa ba, ta yaya za su iya kayar da shi yanzu da ya cika alkawuran kamfen dinsa?”
- Reno Omokri
Omokri ya ce ana yabon manufofin Tinubu
Faston ya bayyana yadda kasashen duniya ke amincewa da manufofin Tinubu, inda ya buga misali da kalaman asusun na da lamuni na Duniya (IMF) na baya-bayan nan.
“A makon da ya gabata ne muka ga IMF a kafafun yada labarai suna cewa a halin yanzu suna zagayawa kasa-da-kasa suna gaya musu cewa idan kuna son sauye-sauyen da ke aiki, to ku koya daga Najeriya."
- Reno Omokri

Source: Facebook
Omokri: 'Talakan Najeriya ya ga sauyi'
Omokri ya kafa hujjar cewa talakan Najeriya yana jin dadi sakamakon manufofin shugaban kasar, inda ya yi ikirarin cewa:
"Tun lokacin da Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, 'yan Najeriya ba su taba tsayawa layi a gidan mai don samun man fetur ba. Ana samun mai a ko’ina. Kuma man fetur ba shi da tsada."
“Wannan ita ce gwamnati ta farko da muka gani tun bayan gwamnatin Yar’Adua, inda farashin man fetur ya sauka har sau da dama. Ba sau daya ba, sau da dama. Saboda haka, suna jin hakan a aljihunsu."
“Kada ku bari wadannan mutanen da ke zuwa majalisar tarayya zanga-zanga su rude ku. Wadannan manyan mutane ne. Suna kokarin kwace mulki ne kawai.”
Ministan Tinubu ya shirya yin murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan ayyuka, David Umahi, ya sha alwashin yin murabus daga mukaminsa.
David Umahi ya sha alwashin cewa zai yi murabus daga mukaminsa idan har aka yi aiki mara inganci a titin hanyar Abuja-Kaduna-Kano.
Tsohon sanatan ya bayyana cewa a shirye yake ya bari masu gwaji su gudanar da bincike kan ingancin aikin da ake yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

