ADC na Fatan Rajistar Mutane Miliyan 14 domin Karfafa 'Yan Adawa
- Babbar jam'iyyar adawa ta ADC ta bayyana cewa tana dab da fara rajistar mutane domin shiga cikinta dumu-dumu a dukkan jihohin Najeriya
- Sakataren jam'iyyar na kasa, Rauf Ogbeni Aregbesola ne ya bayyana haka yayin wani taron manyan 'yan siyasa da ya jagoranta a jihar Oyo
- Tsohon gwamnan jihar Osun ya bayyana cewa suna so su tabbatar da masu gaskiya da kishin kasa sun shiga jam'iyyar domin kawo sauyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Sakataren jam’iyyar ADC, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa jam’iyyar tana son samun akalla mambobi miliyan 14 da za su yi rajista a faɗin ƙasar nan.
Aregbesola ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki na yankin Kudu maso Yamma da aka gudanar a Kakanfo Inn da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Source: Facebook
ADC za ta yi rajistar 'yan jam'iyya
Tsohon gwamnan jihar Osun ya ce jam’iyyar na shirin fara gangamin jan hankalin mambobi da nufin jawo hankalin ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da ba su gamsu da tsarin siyasar da ake ciki ba.
“Burimmu shi ne mu kawo ‘yan Najeriya da suke shirye su yi aiki domin cigaba na gaskiya.
"A wannan karon, muna son mu tantance masu gaskiya daga marasa gaskiya ta hanyar tabbatar da cewa masu ƙwazo da nagarta kaɗai za su shiga jam’iyyar,”
- Inji shi
Jagoran ADC ya ƙara da cewa hasashen yawan mambobin da jam’iyyar ke sa rai a nan gaba yana da yawa, amma za a iya cimma shi idan aka haɗa kai wajen gangamin wayar da kai a matakin ƙasa da ƙananan hukumomi.
Ya ce:
“Zai yi kyau yawan mambobinmu ya kai akalla miliyan 14. Wannan shi ne tsarin da muke ginawa, kuma a shirye muke mu yi amfani da abin da muke da shi domin cimma wannan buri,”

Kara karanta wannan
Atiku ko Obi: El Rufai ya yi maganar wanda zai iya samun tikitin takarar ADC a zaben 2027

Source: Facebook
Jam'iyya ADC ba ta fada da kowa
Aregbesola ya jaddada cewa ba a kafa ADC domin yin yaƙin siyasa da wasu mutane ko jam’iyyun adawa ba, sai dai domin gina tafiyar siyasa mai maida hankali kan hidima ga al’umma.
Ya ce:
“Ba ma yaƙi da kowa. Manufarmu ita ce mu kira jama’a su yi aiki, daga matakin shiyya zuwa jihohi, ƙananan hukumomi da ma mazabu, domin samar wa ‘yan Najeriya sahihin dandalin siyasa,”
A wani sako da kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa a gobe Alhamis, 12 ga Fabrairun 2026 za su kaddamar da rajistar 'yan jam'iyyar.
Manyan ADC sun ziyarci Janar IBB
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jagoranci tawaga da ta hada da manyan ADC zuwa Neja.
Manyan 'yan siyasar da ke karkashin ADC sun gana da tsohon mataimakin shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (Mai ritaya).
Baya ga haka, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya kasance a cikin tawagar Atiku Abubakar duk da cewa dan jam'iyyar PDP ne ba ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
