Nasir El Rufa'i Ya Fito Ya Yi Magana Daga Kasar Waje kan Barazanar Cafke Shi

Nasir El Rufa'i Ya Fito Ya Yi Magana Daga Kasar Waje kan Barazanar Cafke Shi

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yi zargin cewa a nan gaba kadan za a iya yin ram da shi
  • Ya bayyana haka ne yayin da siyasar 2027 ke kara karatowa, inda jam'iyyu suka fara shirin fuskantar zabe
  • Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa a yanzu haka an kama wasu mutanen da ya yi aiki da su a jihar Kaduna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya yi maganar da ke nuna cewa zai iya shiga hannun hukumomin Najeriya.

El-Rufai wanda yana ketare ya bayyana haka ne lura da yadda aka kama wasu daga cikin wadanda suka yi aiki da shi a lokacin da ya ke gwamna a Kaduna.

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi gajeren tsokaci kan rikicinsa da Uba Sani da sabanin Kwankwaso da Abba

Nasir El-Rufa'i dauke da tutar ADC
Nasir El-Rufa'i a wani taron ADC. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Kaduna ya yi magana game da halin da ya ce zai iya shiga ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

Maganar kama Nasir El-Rufa'i a Najeriya

Malam Nasir El-Rufa’i da ke jam’iyyar hamayya ta ADC ya yi ikirarin cewa wasu ‘yan siyasa na komawa jam’iyyar APC mai mulki ko kuma su cigaba da zama a cikinta saboda wasu dalilai na tilas.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara zafi yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

A kwanan nan, El-Rufa’i ya kara tsaurara kalaman suka da yake yi wa gwamnatin Bola Tinubu da jam’iyyar APC.

Da yake magana a wata hira, ya ce duk da har yanzu ba a kama shi ba, amma an kama wasu na kusa da shi, lamarin da ya sa yake ganin shi ma ana iya zuwa kansa nan gaba kadan.

Kara karanta wannan

Zance ya fito: El Rufai ya haska abin da ya jawo sabani tsakaninsa da Tinubu

El-Rufa'i ya ce:

“An kama mutum wajen guda huɗu waɗanda muka yi aiki da su a Kaduna, saboda haka ni ma lokaci ne, ni ma za a neme ni,”

Maganar kama Abubakar Malami

A gefe guda kuma, batun kama tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da shari’ar da ake yi masa sun dauki hankalin jama’a.

Hukumar EFCC ta tuhumi Malami da zargin amfani da mukami ba bisa ka’ida ba da kuma safarar kudi ba bisa doka ba.

Daga bisani kuma an sake cafke shi bisa zargin hannu a ayyukan da suka shafi tallafa wa ta’addanci.

Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami
Tsohon ministan Najeriya da EFCC ta kama. Hoto: Abubakar Malami
Source: Facebook

Malami, wanda ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan adawa da APC, ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.

Ana ganin hakan ne ya sanya El-Rufa'i cewa masu zama a APC suna yin hakan ne saboda tsoron kada a kama su.

Maganar El-Rufa'i kan Akpabio

A wani labarin, kun ji cewa Malam Nasir El-Rufa'i ya yi magana game da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

Akpabio: El Rufa'i ya zargi Shugaban Majalisa da zama alaƙaƙai wajen gyara dokar zabe

Maganar El-Rufa'i ta zo ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya suka matsa lamba game da gyara dokokin zabe.

Tsohon gwamnan Kaduna ya ce ya san Akpabio shekaru da dama da suka wuce, inda ya zarge shi da kawo tsaiko a gyara wata doka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng