Fitacciyar Ƴar Siyasa, Naja'atu Muhammad Ta Kausasa Harshe a kan Siyasar Pantami
- Hajiya Naja'atu Muhammad ta kira Sheikh Isa Ali Pantami da makaryaci saboda ya karbi mukamin minista bayan ya taba sukar siyasa
- Ta bayyana cewa tsarin siyasar Najeriya kama-karya ce kawai domin shugaban kasa ne yake iko da hukumar zabe da jami'an tsaro
- Naja'atu ta tabbatar da cewa Pantami ya kasance yana halartar tarurrukan jam'iyyar ADC, amma wani dalili ya sanya shi yin rajista da APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Fitacciyar 'yar gwagwarmayar siyasa a Arewacin Najeriya, Hajiya Naja'atu Muhammad, ta yi tsokaci game da siyasar Sheikh Isa Ali Pantami.
Hajiya Naja'atu ta kausasa harshe kan tsohon ministan tarayyar, wanda ta kira shi kai tsaye da "makaryaci" saboda wasu karatuttuka da ya yi a baya.

Source: UGC
'Yar gwagwarmayar samar da kyakkyawan shugabancin ta yi maganganu kan Pantami ne a shirin Zauren Ali Jita, wanda mawakin ya wallafa a shafinsa na YouTube a ranar 10 ga Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan
Bayan shekaru 76, kotu ta yi hukunci da gwamnatin Birtaniya ta kashe 'yan Najeriya 21
Mahangar Naja'atu kan siyasar Najeriya
Yayin da take tsokaci game da siyasar Arewacin Najeriya, Naja'atu ta ce:
"SubhanalLah. Yanzu ba siyasa ake yi ba. Ba ma a Arewa ba, a kasar baki daya, bangar siyasa ake yi, watau kama-karya, babu hukuma, kowa yana abin da ya ga dama."
'Yar gwagwarmayar ta yi nuni da cewa, shugaban kasa shi ke da iko kan shugaban hukumar zabe, kuma duk masu ruwa da tsaki a harkar zaben "na cikin aljihunsa."
A cewarta, hakan na nufin sai furar da shugaban kasar ya dama masu ne za su sha, yayin da kuma ta yi korafi a kan yadda ake tura 'yan sanda da sojoji rumfunan zabe.
"Babu dalili, duk duniya ban ga inda aka ce dan sanda da soja sun je wajen zabe ba, sai a Najeriya. Idan aka ce sai an ba ka kudi za ka yi zabe, to ina dimokuradiyyar? Kama karya ce."
- Hajiya Naja'atu Muhammad.
Ta yi ikirarin cewa, a Najeriya akwai doka, amma mai kaddamar da dokar ne babu, tana mai cewa wanda zai kaddamar da dokar ma ya fi saba wa doka.
'Pantami makaryaci ne' - Naja'atu
Da aka tabo batun siyasar Sheikh Pantami, 'yar gwagwarmayar ta kausasa harshe da cewa:
"Pantami makaryaci ne. Ni na ce maku, Pantami ya na fantama karya. Ya mallaki idonsa ya mallaki harshensa."
Hajiya Naja'atu ta ce Pantami ya na kuka, yana la'antar siyasa, yana tir da karbar mulki amma a karshe ya zo ya karbi mukamin minista, tana mai cewa:
"Ka san akwai 'yan Ahlus Sunnah, akwai 'yan Ahlit Talauci, suna nan da yawa. In suna cikin talauci da tsilan wando, sai su rika kira maka Sunnah. Amma da sun samu sun yi kwana kwana, sun je su ma sun sanya hannunsu a cikin haram sai ka ga wandonsu ya koma kamar tantabara, har yana jan kasa.
"Ko da ya karbi ministan, karya yake, bai taba yin APC ba. Ya ce wai shi siyasar da ya yi ta farin kaya ce."

Source: Twitter
'Pantami ya yi ADC tare da mu' - Naja'atu
Hajiya Naja'atu ta kuma yi nuni da cewa, da can Sheikh Isa Pantami yana tare da ADC, kuma har yana zuwa tarurrukan jam'iyyar.
Ta yi ikirarin cewa Pantami ya gudu ne daga jam'iyyar ADC lokacin da ya ga an fara kama wasu mambobinta kamar Abubakar Malami domin gudun kada a taba shi.
"Ina mai tabbatar maka da cewa ni na san Pantami yana zuwa tarurrukanmu. Yana ganin an kama Malami, sai ya yi maza maza ya gudu, kila ko sun fara dan yakusarsa shi ma.
"Saboda ni ba na damuwa da ire irensu Pantami."
- Hajiya Naja'atu Muhammad.
Kalli bidiyon tattaunawar a nan kasa:
Pantami ya ki amsa tayin Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Farfesa Isa Ali Pantami ya sabunta rajistar zama dan jam'iyyar APC inda ya fadi gaskiyar alakarsa da Shugaba Bola Tinubu.
Malamin ya bayyana cewa har yanzu yana ba Tinubu shawarwari kuma yana karba saboda kokarinsa a nasarar shugaban kasar a zaben 2023.
Pantami ya kuma bayyana cewa bai karbi tayin mukamai uku da Tinubu ya yi masa ba, yayin da ake zargin zai nemi takarar gwamnan jihar Gombe a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

