Kullin Siyasa: Atiku da Gwamnan PDP Sun Sa Labule da Tsohon Shugaban Najeriya
- Atiku Abubakar da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo sun ziyarci tsohon shugaban Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida
- Rahoto ya nuna cewa Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa, shi ne ya fara isa tare da sa labule da IBB kafin karasowar Gwamna Makinde
- Duk da babu wata sanarwa a hukumance kan abin da suka tattauna, amma ana hasashen taron ya maida hankali kan abubuwan da suka shafi kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Minna, Niger State - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya isa gidan tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Atiku ya kai ziyara gidan Janar IBB mai ritaya ne a yau Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026 da tsakar rana, kuma daga zuwa ya sa labule da tsohon shugaban kasar.

Source: Twitter
Atiku Abubakar ya dura gidan IBB a Minna
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Atiku, wanda ya isa gidan IBB da ke kan tsauni da kusan misalin ƙarfe 1:00 na rana, ya shiga taron sirri kai tsaye da tsohon shugaban.
Bayanai daga birnin Minna sun nuna cewa jiga-jigan biyu sun tattauna muhimman batutuwan siyasa da suka shafi ƙasar nan.
Me Atiku da IBB suka tattauna a kai?
Majiyoyi sun bayyana cewa tattaunawar ta fi karkata ne kan gyaran dokokin zaɓe, musamman batun tura sakamakon zaɓe ta na’ura kai tsaye daga kowace rumfar zabe a Najeriya
Sauran abubuwan da Atiku ya tattauna da IBB sun hada da sababbin dokokin haraji, da sauran batutuwa masu muhimmanci ga halin da siyasar Najeriya ke ciki a yanzu.
Janar Babangida ya shafe shekaru takwas yana mulkin Najeriya daga 1985 zuwa tsakiyar 1993.
Gwamna Makinde ya isa gidan IBB
Kimanin mintuna 40 bayan fara taron IBB da Atiku Abubakar, Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya isa gidan tsohon shugaban kasa kuma kai tsaye ya shiga wannan taron na sirri.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027
Rahoton The Nation ya ce ana sa ran ko dai Atiku Abubakar ko kuma tsohon shugaban ƙasar, Janar Babangida, za su yi wa manema labarai bayani bayan kammala wannan ganawa.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce da sukar Majalisar dattawa kan matakin da ta dauka na kin amincewa da bukatar tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye.

Source: Twitter
Wannan lamari ya haddasa zanga-zanga, wacce aka ga manyan mutane sun shiga ciki har da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa batun gyaran dokar zaben Najeriya da sababbin dokokin haraji na cikin muhimman abubuwa da ganawar Atiku da IBB ta maida hankali a kai.
IBB ya karbi bakuncin Obasanjo a Minna
A baya, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a jihar Neja.
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan isowarsa Minna, wasu jami'ai daga gidan gwamnatin Jihar Neja ne suka tarbi Obasanjo kafin ya nufi gidan tsohon shugaban.
Rahoto ya nuna cewa ganawar ta gudana cikin sirri, inda Obasanjo da Babangida suka shafe kusan mintuna 30 suna tattaunawa ba tare da bayyana wa jama’a abin da suka tattauna ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
